Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

  • Wani tsohon minista ya bayyana rashin hadin kan mutanen kudu maso gabas a matsayin matsalarsu
  • Ya bayyana cewa, suna da kudi, kuma sun watsu a kowane sashe na Najeriya, amma basu da hadin kai
  • Ya kuma bayyana cewa, babu wanda ya fi cancantar gadon kujerar shugaba Buhari a 2023 fiye da Bola Tinubu

Wani tsohon Ministan Ayyuka a Najeriya, Adeseye Ogunlewe, ya ce Kudu maso Gabas ba za su iya samar da shugaban kasar Najeriya na gaba ba saboda ba su da hadin kai.

Ya fadi hakan ne yayin wani shirin Arise TV mai suna 'The Morning Show' a ranar Laraba 11 ga watan Agusta, Punch ta ruwaito.

A cewarsa, babu wani dan takarar da ya fi dacewa ya jagoranci kasar nan a 2023 fiye da tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu - wata sanarwa da Bode George, memba na kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, wanda shi ma ya kasance a cikin shirin.

Kara karanta wannan

Idan zaben 2023 ya zo, Bola Tinubu bai da satifiket da zai nuna ya yi karatu inji Bode George

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023
Adeseye Ogunlewe | Hoto: newsexpressngr.com
Asali: UGC

Ya yi ikirarin cewa rashin iya jagoranci da rashin hadin kai zai yi tasiri kan duk wani dan takarar shugaban kasa na Kudu maso Gabas.

Ya ce:

“Wasu rukunin mutane da suka dace, su ne mutanen Kudu maso Gabas amma suna da matsalar shugabanci.
“Suna da baiwar da suka bazu ko'ina a cikin Najeriya kuma suna iya samun kuri’u da yawa, amma sun basu da hadin kai kwata-kwata. Mutumin Imo, dan Enugu, dan Ebonyi ba za su saurari kansu ba.
“Suna da kudi. Idan suka zauna suka tattara abin da za su iya bayarwa, suna da kudi fiye da kusan kowa a Najeriya.
"Amma kun taba ganin mutum daya daga kudu maso gabas ya ce 'Ina sha'awar shugabancin kasa, zan fara kamfen a duk fadin Najeriya nan da nan, ku tara mani kudi?' Kuma ya yi tasiri ga tsarin jam'iyya?"

Yahaya Bello ne matashin dan takarar da zai iya gyara Najeriya, in ji wani sanatan Kogi

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa take da tsauri kan tafiya kasar waje

Sanata Smart Adeyemi (APC – Kogi ta yamma) ya bayyana Yahaya Bello a matsayin dan takarar shugaban kasar Najeriya da ya fi cancanta da gadon shugaba Buhari a zaben 2023, kuma ya daga Najeriya ta fuskar karfin tattalin arzikin duniya.

Sanatan na Kogi ya bayyana gwamnan na Kogi a matsayin gwamna matashi mai dimbin kuzari, da basirar ilimi da sanin makamar aiki tare da tarihi mai kima, ya kara da cewa yana da abin da zai kai kasar nan zuwa tudun na tsira, Daily Sun ta ruwaito.

Da yake rokon ‘yan Najeriya da su yi la’akari da burin zama shugaban kasa na Gwamna Bello, Sanata Adeyemi ya ce idan aka ba shi dama gwamnan zai hada da nasarorin gwamnatin Buhari.

Bayan Fitowa Daga Taro, Gwamnonin APC Sun Bayyana Matakin da Suka Dauka a Kan Shugaban APC Mai Mala Buni

A wani labarin, Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki sun kaɗa kuri'ar amincewa da kwamitin rikon kwarya wanda takwaransu gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yake jagoranta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

A bari yan kabilar Igbo su balle kawai mu huta, Tsohon Jakadan Najeriya

Gwamnonin sun bayyana cewa hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaɓen gwamnan jihar Ondo ya nuna cewa kwamitin na kan doka.

Gwamnonin sun yi wanna jawabin ne a taron da suka gudanar ranar Litinin domin tattauna matsalolin da suka taso a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel