Kocin Barcelona ya bayyana ‘dan wasan da zai maye gurbin da Lionel Messi ya bari

Kocin Barcelona ya bayyana ‘dan wasan da zai maye gurbin da Lionel Messi ya bari

  • Ronald Koeman yana ganin Barcelona za ta kai labari duk da Lionel Messi ya tashi
  • Kocin kungiyar ya ci buri a kan irinsu Antoine Griezmann su maye gurbin Tauraron
  • Akwai lokacin da ake jita-jitar ba a shiri tsakanin Griezmann da Messi a Barcelona

Barcelona - Kocin kungiyar Barcelona, Ronald Koeman, ya yi magana a kan yadda za su samu kansu bayan tauraron ‘dan wasan nan, Lionel Messi ya tashi.

Ronald Koeman ya na sa ran cewa za a samu wani wanda zai maye gurbin da Lionel Messi ya bari a cikin ‘yan wasan da suke buga wa kungiyar kwallon.

Gerard Pique ya bayyana cewa zuciyar ‘yan wasan Barcelona ya mutu a dalilin tashin Lionel Messi.

Metro ta rahoto cewa idanun Ronald Koeman suna kan ‘dan wasa gabansa, Antoine Griezmann wanda ya yi kwallo na shekaru biyu tare da Messi a kungiyar.

Rahoton yace amma duk da haka, mai horas da ‘yan wasan, Koeman yana ganin Antoine Griezmann zai iya bin sahun tsohon abokin aikinsa watau Messi.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Ba a ga daman ceto yaran da ake sace wa bane inji Tsohon Ministan Buhari

Mu na da yara da sabbin 'yan wasa - Koeman

“Duk da ban-kwana da aka yi da Leo Messi, muna shirya wa sabuwar kakar da za a shiga.”

Lionel Messi da Antoine Griezmann
Lionel Messi da Antoine Griezmann a wani wasa Hoto: www.skysports.com
Asali: UGC

“Da ‘yan wasanmu da ke nan, da cefanen da mu ka yi, mu na kuma da kananan ‘yan wasa masu tashi, wanda tun asali da su wannan kulob din ya dogara.”
“Akwai bukatar ya zama mu na da ‘dan wasan da ya fi kowa, amma ka da mu canza salonmu, Griezmann ya buga wannan lambar, ya kuma tabuka."

Kungiyar Barcelona babu Lionel Messi

Kamar yadda jaridar ta rahoto, Barcelona za ta gamu da kalubale a shekarar 2021/22 ganin cewa ta rabu da Messi wanda ya yi shekara da shekaru ya na tashe.

Bugu da kari, sabon ‘dan wasan Argentina, Sergio Aguero ba zai fara buga wasa ba sai nan da wasu ‘yan makonni, a sakamakon wani sabon rauni da ya samu.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Barcelona sun kai kara da nufin haramtawa PSG daukar Lionel Messi

Kungiyar ta gaza ba tauraron ‘dan wasan sabon kwantiragi ne saboda matsalar rashin kudi, hakan ta sa ya koma kungiyar Paris Saint-Germain a kasar Faransa.

Akwai lokacin da tsohon dillalin, Griezmann, Eric Olhats yace Lionel Messi ya hana tsohon ‘dan wasan na Athletico Madrid sake wa, amma shi ya musanya hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel