Mun fidda mutum milyan 10 daga cikin talauci a shekaru shida, Gwamnatin tarayya

Mun fidda mutum milyan 10 daga cikin talauci a shekaru shida, Gwamnatin tarayya

  • Gwamnatin Buhari ta lashi takobin fidda yan Najeriya milyan 100 daga cikin talauci nan da 2030
  • Ministar tattalin annoba da tallafi, Sadiya Farouq, ta bayyana adadin da aka fiddar kawo yanzu
  • A cewarta, an rage hanya tun da an fitar da mutum milyan 10 cikin shekaru 6

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fidda sama da yan Najeriya milyan 10 daga cikin bakin talauci ta shirye-shiryen tallafi da jin kai ta NSIP, cewar Minista Sadiya Farouq.

Hajiya Sadiya Umar Farouq, wacce take rike da kujerar Ministar tattalin annoba da tallafi, ta sanar da hakan ne a taron lissafin adadin mutanen dake fama da talauci a kasashe masu tasowa.

Mun fidda mutum milyan 10 daga cikin talauci a shekaru shida, Gwamnatin tarayya
Mun fidda mutum milyan 10 daga cikin talauci a shekaru shida, Gwamnatin tarayya Hoto: @sadiya_farouq
Asali: Facebook

Magance talauci

A jawabin da mai magana da yawunta, Nneka Ikem Anibeze, ya saki kuma Legit.ng ta gani, ya ruwaito ta tana cewa:

"Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu nasarar karfafa mutum sama da milyan goma da kuma tsamosu daga talauci ta shirye-shiryen gwamnatin masu yawa, wanda ya hada da shirin tallafi na NSIP.

Kara karanta wannan

Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai

"An yi wadannan abubuwa ne saboda adadin yan Najeriya ya kai milyan 200."

Farouq ta kara da cewa gwamnatin tarayya zata hada kai da kamfanoni masu zaman kansu domin bibiyan mutanen dake fama da talauci don taimaka musu da kuma tsamosu daga ciki.

Ta godewa bankin duniya, UNICEF, da kuma kungiyoyin tallafi bisa gudunmuwan da suke badawa wajen ganin an yakice talauci a duniya nan da 2030.

Tallafin rayuwa: Mun kashe wa ’yan Najeriya miliyan 11 Dala miliyan 415

Ministar Jin Kai da Kula da Bala’o’i, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa ’yan Najeriya miliyan 11 ne ya zuwa suka ci gajiyar Shirin Tallafa wa da Ci gaban Al’umma (CSDP) a jihohi 29 inda aka kashe Dala miliyan 415 a kai.

Ta bayyana cewa ta hanyar shirin an gina azuzuwa guda 5,764 da cibiyoyin kiwon lafiya guda 1,323 a wasu kananan ayyuka guda 4,442 inda wasun aka yi musu kwaskwarima yayin da aka gudanar da wasu kananan ayyukan guda 16,166 a kauyuka 5,664.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

Sun ta rahoto cewa ministar ta fadi hakan a ranar Laraba a Abuja yayin wani taro kan shirin na CSDP, inda ta ce an faro shirin ne tun a 2009, sannan ya kunshi harkokin rayuwar yau da kullum guda takwas — ilimi da kiwon lafiya da ruwa da sufuri da lantarki da zamantakewar yau da kullum da muhalli da raya karkara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel