Mutane 10 sun jikkata yayin da sojoji suka dakile wani kazamin rikici a Filato

Mutane 10 sun jikkata yayin da sojoji suka dakile wani kazamin rikici a Filato

  • Jami'an sojoji sun yi nasarar dakile wani mummunan rikici da ka iya kazanta a karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jihar Filato
  • Rikicin dai ya barke ne a tsakanin ‘yan asalin yankin da Hausawan da suka yi kaka-gida
  • Lamarin wanda ya afku a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, ya yi sanadiyar jikkata wasu mutane 10

Jos, Filato - Matakin gaggawa da jami'an tsaro suka dauka a ranar Litinin ya dakile wani lamari da ka iya zama kazamin karo tsakanin ‘yan asalin yankin da Hausawa mazauna karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

An shiga halin fargaba a jihar bayan hare-haren da makiyaya suka kaddamar a kananan hukumomin Bassa da Riyom, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama da kone-konen gine-gine.

Makiyayan sun kuma lalata manyan gonaki na 'yan asalin yankin.

Mutane 10 sun jikkata yayin da sojoji suka dakile wani kazamin rikici a Filato
Matakin gaggawa da sojoji suka dauka ne ya takaita lamarin Hoto: The Nation
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rahoto cewa matakin gaggawa da jami’an Operation Safe Haven (OPSH) suka dauka ya hana rikicin ya rikide zuwa na zub da jini.

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamnatin Buhari ta ware wa 'yan sanda kudin sayen man fetur

Wata majiya da ke kusa da wurin da abin ya faru a Naraguta ta bayyana cewa Hausawa da sanyin safiyar Litinin sun gano wata hanya da karkatar da ita zuwa inda ake binne Musulmi a Yelwa Zangam a cikin garin.

Saboda haka sai suka yi kokarin hana wadanda ke tona hanyar ruwar da ke kusa da makabartar.

An tattaro cewa an samu gagarumin saɓani, wanda ya ja hankalin sauran mutane a cikin garin, wanda ya haifar da tashin hankali inda mutane goma suka sami raunuka daban-daban.

An kuma tattaro cewa jami’an OPSH, waɗanda suka isa lokacin sun takaita lamarin daga tabarbarewa.

Kansilan gundumar, Hon. Yusuf Ali, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi zargin cewa 'yan asalin yankin na kokarin karkatar da wata hanya kusa da wurin binne Musulmai zuwa wani wuri mafi aminci sai Hausawa suke ganin hakan a matsayin wata dabara ce ta kutsawa cikin makabartar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Filato ASP Gabriel Ubah ya shaida wa jaridar The Nation cewa:

Kara karanta wannan

Akalla Mutum 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Fatattaki Yan Bindiga a Kaduna

“Ina sane da lamarin amma har yanzu ban samu cikakken bayani ba. Da zaran na samu, ba zan jinkirta ba ku ba.”

Rikici a Plateau: An kashe mana mutum 70 cikin kwanaki 4, Mutan Irigwe

A wani labarin, mun ji cewa akalla mutum 70 ne aka ce sun rasa rayukansu a garin Jebbu Miango da Kwall na karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau sakamakon harin yan bindiga.

Kaakin kungiyar cigaba Irigwe, Davidson Malison, ya bayyana hakan ranar Alhamis yayinda yan ziyara suka ziyarci wajen da aka kai harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel