WAEC Ta Sanar da Sabuwar Ranar da Za'a Fara Rubuta Jarabawar WASSCE 2021

WAEC Ta Sanar da Sabuwar Ranar da Za'a Fara Rubuta Jarabawar WASSCE 2021

  • Hukumar WAEC ta bayyana cewa za'a fara jarabawar bana ranar 16 ga watan Agusta
  • Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban ofishin hukumar a Najeriya, Mr. Patrick Areghan, ya fitar
  • Yace jadawalin jarabawar ya nuna cewa za'a shafe makwanni bakwai ana gudanar da jarabawar a Najeriya

Lagos - Hukumar dake shirya jarabawar fita daga sakandire a nahiyar Africa ta yamma (WAEC) ta sanar da ranar 16 ga watan Agusta a matsayin ranar da za'a fara jarabawar bana 2021, kamar yadda punch ta ruwaito.

Shugaban hukumar a Najeriya, Mr. Patrick Areghan, shine ya fitar da wannan sanarwar a Lagos ranar Talata.

Ofishin WAEC a Najeriya dake Lagos
Da Duminsa: WAEC Ta Sanar da Sabuwar Ranar da Za'a Fara Rubuta Jarabawar WASSCE 2021 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sanarwar tace:

"Duba da jadawalin karshe da aka fitar na kasa-da-kasa, za'a gudanar da jabawar ta bana WASSCE 2021 a faɗin nahiyar Africa ta yamma daga Litinin 16 ga watan Agusta zuwa Jumu'a 8 ga watan Oktoba, 2021."
"Saboda hakane za'a karkare jarabawar a Najeriya ranar 30 ga watan Satumba. Za'a shafe tsawon mako 7 ana gudanar da jarabawar a Najeriya."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ba za'a tsige Uche Secondus daga jagorancin PDP ba, Tambuwal

Makarantu nawa ke rubuta WAEC a Najeriya?

Mr. Areghan ya bayyana cewa kididdiga ta nuna cewa makarantun sakandire dubu 19,425 ne a faɗin Najeriya suka cancanci zana jarabawar.

Vanguard ta ruwaito Areghan yana cewa:

"Makarantun sun haɗa da na gwamnati guda dubu 8,052 da kuma masu zaman kansu 11,373 a faɗin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja."

Meya hana gudanar da jarabawar a Mayu/Yuni?

Dangane da dalilin rashin gudanar da jarabawar a watan Mayu da Yuni kamar yadda aka saba, Shugaban WAEC a Najeriya yace bukatar samar da tsarin jarabawar na ƙasa da ƙasa, annobar korona, na daga cikin dalilan ɗage ta.

Ya kuma kara da cewa an bukaci a saita jarabawar da yadda tsarin karatun sakandiren Najeriya ke tafiya, da kuma bukatar dage jarabawar da gwamnatin tarayya ta nema duk suna cikin manyan dalilai.

Daga karshe shugaban WAEC ya kara jaddada cewa hukumar ba zata lamurci duk wani salo na satar amsar jarabawar ba.

Kara karanta wannan

Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai

A wani labarin kuma sabon rahoton da aka fitar na jerin masu kudin duniya ya nuna cewa Dangote ya koma na 117

Rahoton ya bayyana cewa Aliko Dangote, shugaban kamfanin 'Dangote Group' ya mallaki dukiyar da takai dalar Amurka biliyan $17.8bn.

Wanda yafi kowa kuɗi a duniya a cewar rahoton shine Elon Musk, haifaffen ƙasar Africa ta kudu, wanda ya mallaki dalar Amurka biliyan $194bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel