Bincike: Nan gaba kadan maza za su rasa matan da za su aura saboda wasu dalilai

Bincike: Nan gaba kadan maza za su rasa matan da za su aura saboda wasu dalilai

  • Bincike ya nuna nan gaba maza za su rasa matan da zasu aura saboda karancin mata a duniya
  • Wannan na zuwa ne bayan gudanar da wani bincike kan kasashe 204 a fadin duniya baki daya
  • Rahoton ya bayyana irin matsalar da maza za su shiga matukar ba a nemi mafita kan wannan ba

Wani bincike kan alkaluman jinsi a duniya ya gano cewa wasu matakai da mutane ke dauka a kan haihuwa za su kawo karancin mata a duniya a nan gaba.

Rahoton binciken da cibiyar lafiya ta BMJ Global Health ta gudanar kan bambanci tsakanin jinshi, ya nuna son haihuwar ’ya’ya maza da kuma al’adar kyamar haihuwar mata sun sa ana yawan zubar da cikin ’ya’ya mata ko kashe jarirai mata a wasu kasashe.

Binciken da cibiyar ta gudanar a wasu kasashe 204 ya nuna daga shekarar 1979 zuwa 2017 an kashe jarirai mata ko an zubar da cikinsu sau miliyan 45, in ji Aminiya.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

Sakamakon binciken ya ce a shekarar 1970 da ’yan kai, jarirai maza da aka haifa a Kudancin Turai da Asiya sun fi mata, kasashen Indiya da Pakistan kuma ke da kashi na 95 cikin 100 na jarirai mata da aka zubar da cikinsu ko ake kashewa.

Marbucin rahoton, Dokta Fengqing Chao, ya ce a halin yanzu, maza na fama da karancin matan da za su aura a wasu daga cikin kasashen da abin ya shafa.

Bincike: Nan gaba kadan maza za su rasa matan da za su aura saboda wasu dalilai
Aure a duniyar dan adam | Hoto: huffpost.com
Asali: UGC

Rahoton ya ce Najeriya da Pakistan na daga cikin kasashen da nan gaba maza za su iya fin mata yawa, amma abin zai yi sauki bayan shekara 20 masu zuwa.

Dokta Chao ya ce daga yanzu zuwa shekarar 2030 akwai yiwuwar rasa jarirai mata 4.7 kuma illar ta wuce batun rashin samun matar aure.

Ya ci gaba da cewa idan ba a yi wa tufkar hanci ba, nan gaba a cikin ko wadanne maza uku, mutum daya ne zai samu matar da zai aura.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Kutsa Wurin Ibada Sun Hallaka Babban Malami Yana Tsaka da Addu'a

Don haka, a cewar rahoton:

“Akwai bukatar yin dokoki da za su tabbatar da daidaiton jinsi domin magance karancin abokan aure.
“Karancin mata a cikin al’umma na iya haifar da miyagun dabi’u da tashin hankali da kuma kawo cikas a zamantakewar al’umma.”

Muna matuƙar buƙatar mazajen aure, ƴan matan Gombe sun koka

A wani lamari mai kama da wasan kwaikwayo, wasu mata marasa aure a jihar Gombe sun yi kukan neman taimako kan rashin samun mazajen aure.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa mummunan lamarin ya ci gaba tsawon wasu shekaru a yankin arewa maso yammacin kasar, inda ta kara da cewa daruruwan mata marasa aure karkashin jagorancin Suwaiba Isa sun mamaye jihar Zamfara.

Sun yi hakan ne don zanga-zangar rashin samun mazajen aure ga kimanin su 8,000 a watan Satumban 2018.

Legit.ng ta tattaro cewa sarkin Yarbawa a Gombe, Abdulrahim Alao Yusuf, ya ce kashi 60% na mutanen da ba ‘yan asalin jihar bane sun fito ne daga yankin kudu maso yammacin kasar.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun yi kakkausan martani kan kotun Amurka kan batun Abba Kyari

Daya daga cikin mazauna jihar Gombe, Godiya Adamu, ta ce shekarunta 35, har yanzu ba ta samu miji ba, tana mai dora alhakin halin da ake ciki kan rashin samun namijin da ke son aure da gaske.

Ta bayyana cewa ta yi soyayya na kimanin shekaru biyar ba tare da sakamako mai ma'ana ba kafin daga baya ta hakura.

Ta ce:

“Me zan yi? Ba zan iya cusa kaina ga maza ba idan ba su zo ba. A iya sani na, rayuwa na ci gaba da miji ko babu miji."

Wata Bafulatana, mai suna Amina, ta ce matsalarta ita ce ta yi karatu, tana mai cewa ta gano cewa yawancin maza a arewa ba sa son auren mata masu ilimi.

Amina ta lura:

“Wataƙila saboda suna ganin ba abu mai sauƙi ba ne a gare su su juya irin wannan matar son ransu. Don haka a wurina, zaɓin shi ne na ci gaba da zama ba aure sannan na zamo uwa da uba ga yarana.”

Kara karanta wannan

Da duminsa: Annobar Korona ta barke a sansanin NYSC na jihar Gombe

Wannan fitsara ne: Malami ya yi tsokaci kan shigar da amaryar Yusuf Buhari tayi

A wani labarin na daban, Babban Malamin addinin Islama, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya yi tsokaci game da shigar da Zahra Bayero; amaryar Yusuf Buhari, yana mai nuna takaicin yadda 'ya'yan musulmai suka baci da shigar nuna tsiraici.

A makon nan wasu hotuna suka watsu a kafafen sada zumunta, wadanda ke nuna Zahra Bayero, budurwar da dan shugaban kasa Buhari zai aura sanye da wasu kaya masu nuna wane bangare na jikinta.

Wannan shiga da tayi ya jawo cece-kuce, yayin da mutane da dama suka nuna damuwarsu da cewa, wannan shiga bata yi dace da addinin Islama ba, kamar yadda budurwar take musulma.

Malamai a bangare guda, sun yi tsokaci kan lamarin, inda shahararren malami Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya yi tsokaci mai tsoratarwa kan wannan shiga.

Nasihar malamin bata tsaya kan Zahra kadai ba, malamin ya yi kira ne ga dukkan masu irin wannan shiga, yana mai tuna yadda ake samun 'ya'yan manya a kasar nan da irin wannan dabi'a.

Kara karanta wannan

Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

A jiya Laraba 4 ga watan Agusta, malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook inda Legit Hausa ta gano yana cewa:

"1. Lalle irin yadda amare 'ya'yan musulmi suke yin shiga ta nuna tsiraici a mahangar Musulunci sannan kuma su dauki hotunansu cikin wannan shiga ta fitsara su watsa wa Duniya, abin takaici ne matuka. Kuma abu ne da zai iya jawo hushin Allah a kan al'ummar Kasa...

Asali: Legit.ng

Online view pixel