Gwarazan Sojoji Sun Yi Gumurzu da Yan Boko Haram, Sun Ragargaje Su a Borno

Gwarazan Sojoji Sun Yi Gumurzu da Yan Boko Haram, Sun Ragargaje Su a Borno

  • Sojojin sun ɗauki matakin gaggawa a kan wasu mayakan Boko Haram da suka yi yunkurin kai hari Damboa
  • Dakarun sojin sun sakar musu ruwan wuta wanda yasa dole yan ta'adɗan suka tsere daga fafatawar
  • Kakakin rundunar sojin ƙasa, Onyema Nwachukwu, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar

Borno - Rundunar sojin ƙasa tace sojoji sun dakile yunkurin yan ta'adda na kai hari garin Damboa a jihar Borno ranar Lahadi, kamar yadda punch ta ruwaito.

Rahoton channels tv ya bayyana cewa gwarazan sojin sun ci karfin yan ta'addan bayan dogon musayar wuta, wanda hakan yasa suka tsere.

Kakakin rundunar ta ƙasa, Onyema Nwachukwu, a wani jawabi da ya fitar yace maharan sun kone motocin jami'an sa kai JTF guda biyu yayin fafatawar.

Ya kara da cewa a halin yanzun sojoji sun bazama nemo yan ta'addan waɗanda suka tsere.

Jami'an rundunar sojojin Najeriya
Gwarazan Sojoji Sun Dakile Yunkurin Wata Tawagar Yan Ta'adda Na Kai Hari Jihar Borno Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wani sashin jawabin yace:

"Dakarun sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wani yunkurin kai hari garin Damboa da safiyar Lahadi, wanda mayakan Boko Haram/ISWAP suka so kaiwa."

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Ragargaji Yan Bindiga Ta Sama da Kasa a Kaduna, Sun Kashe Sanannun Yan Ta'adda

"Yan ta'addan sun yi kokarin afkawa garin amma sai suka haɗu da ruwan wuta daga jami'an sojoji da suke a ankare."
"Yan ta'addan sun yi yunkurin shiga garin da adadi mai yawa na mayaka wasu tafe a kafa wasu kuma a kan motoci. Amma ba su ji da daɗi ba a hannun sojoji yayin da dole tasa su tserewa cikin mawuyacin hali na raunukan harbi."

Sojoji sun bazama binciken yan ta'addan

Kakakin sojojin ya bayyana cewa sojojin ba su tsaya nan ba domin yanzun haka sun bazama nemo waɗanda suka kai wannan harin.

Jawabin ya cigaba da cewa:

"Abu mara daɗi shine an kona motoci biyu na jami'an tsaron sa kai (JTF) yayin artabun. An yabawa sojojin Operation haɗin kai bisa namijin kokarin da suke yi na maida martani idan an kawo hari."
"Hakanan an yi kira gare su kar subar wata kofa ga yan ta'addan waɗanda suke fama da matsin lamba na ruwan bama-bamai da sojojin sama suke yi a kansu."

Kara karanta wannan

Akalla Mutum 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Fatattaki Yan Bindiga a Kaduna

A wani labarin kuma Murna Ta Koma Ciki yayin da Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Yan Bikin Aure da Dama a Kwara

Aƙalla mutum 27, cikinsu har da yan bikin aure 7, Fasto da matarsa aka sace a harin yan bindiga biyu kan hanyar Kwara-Ekiti ranar Asabar da yamma.

Majiyar yan sanda ya nuna cewa yan bindigan sun yi awon gaba da mahalarta ɗaura aure 7 yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Ilorin daga Kwara.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel