Da Dumi-Dumi: Shahararren Dan Kasuwa, Okunbo, Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Shugaba Buhari Ya Yi Jimami

Da Dumi-Dumi: Shahararren Dan Kasuwa, Okunbo, Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Shugaba Buhari Ya Yi Jimami

  • Babban ɗan kasuwa haifaffen jihar Edo, Captain. Wells Okunbo, ya rigamu gidan gaskiya yana da shekara 63
  • Okunbo ya rasu ne a wani asibiti da ba'a bayyana ba a Landan bayan fama da rashin lafiya
  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi ta'aziyyar wannan rashi tare fatan alkairi ga Captain

London, England - Babban attajirin ɗan kasuwa kuma haifaffen jihar Edo, Capt. Idahosa Wells Okunbo, ya rigamu gidan gaskiya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Okunbo, wanda sirikin babban basaraken Wari ne, ya kwanta jinyar rashin lafiya a wani asibiti da ba'a bayyana ba a birnin Landan.

This day ta ruwaito cewa ɗan kasuwan mai kimanin shekara 63 a duniya ya kwanta dama ne ranar Lahadi da safe yayin da yake fama da cutar da ta shafi ciwon daji.

Capt. Idahosa Wells Okunbo
Da Dumi-Dumi: Shahararren Dan Kasuwa, Okumbo, Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Shugaba Buhari Ya Yi Jimami Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Okunbo tsohon matukin jirgin sama ne a kamfanin yan kasuwa kuma shugaban kamfanoni da dama da suka haɗa da kamfanin Ocean Marine Security Limited.

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake yunkurin kashe ni sau biyu - Kakakin IBB Afegbua

Idahosa Wells Okunbo, ya mutu ya bar mata ɗaya da kuma 'ya'ya da dama.

Shugaba Buhari ya yi ta'aziyya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin, abokansa da makusanta.

Shugaba Buhari, a wani jawabi da kakakinsa, Femi Adesina, ya fitar ranar Lahadi, ya yi kira ga masu jimamin rasuwarsa musamman mutanen jihar Edo su yi koyi da halayensa na kwarai.

A jawabin shugaba Buhari yace:

"Gudummuwa da hannun jarin da Okonbo ya zuba a ɓangaren albarkatun man fetur, samar da wutar lantarki, sadarwa da sauransu sun taimaka matuka gaya wajen cigaban tattalin arzikin Najeriya, tare da samarwa iyalai da dama hanyoyin samun abinci.

Daga karshe, shugaba Buhari, ya yi addu'ar fatan alkairi ga marigayi, Capt. Idahosa Wells Okunbo.

A wani labarin kuma Gwamna Zulum Ya Bayyana Yadda Yake Farin Ciki da Yan Boko Haram/ISWAP Suke Tuba a Borno

Gwamnatin jihar Borno ta bayyana jin daɗinta yayin da ake kara samun karuwar yan ta'adda suna tuba su mika makamansu ga sojoji a jihar.

Kara karanta wannan

2023: IBB ya bayyana abubuwa guda 8 da suka zama dole wanda zai gaji Buhari ya kasance da su

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Borno, Alhaji Babakura Abba-Jato, shine ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala taron tsaro a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel