Dalla-dalla: Obasanjo ya lallaba Kwatano domin nemawa Igboho mafaka da afuwa

Dalla-dalla: Obasanjo ya lallaba Kwatano domin nemawa Igboho mafaka da afuwa

  • An gano yadda tsohon shugaban kasar Najeriya ya kai ziyara a boye zuwa jamhuriyar Benin a makon farko na watan Augustan 2021
  • Labarai sun bayyana akan yadda tsohon shugaban kasar ya biya Zanzibar, wani tsibiri dake Tanzania a ranar 1 ga watan Aungusta kafin ya wuce Benin
  • Ya je jamhuriyar Benin din ne don yin ta’aziyya ga Nicephore Saglo bisa mutuwar matarsa wata majiyar kuma tace akan lamarin Igboho yaje

Cotonou - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasabjo ya kai ziyara jamhuriyar Benin a makon farko na Augustan 2021 kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Manyan majiyoyi sun sanar da theCable cewa sai da tsohon shugaban kasar ya biya ta tsibirin Zanzibar dake Tanzania a ranar 1 ga watan Augusta kafin ya wuce Benin din.

Dalla-dalla: Obasanjo ya lallaba Kwatano domin nemawa Igboho afuwa
Dalla-dalla: Obasanjo ya lallaba Kwatano domin nemawa Igboho afuwa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Obasanjo yaje ziyarar ta'aziyya

Ya kai ziyarar ne don yin ta'aziyya ga Nicephore Soglo wanda bai dade da rasa matarsa Roseline Soglo ba. Roseline ta rasu ne a ranar 25 ga watan Yuli tana da shekaru 87 a Cotonou.

Kara karanta wannan

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

Soglo tsohon Shugaban kasar Jamhuriyar Benin ne daga 1991 zuwa 1996.

TheCable ta fahimci tsohon shugaban kasa Obasanjo da Sangolo sun rike abotarsu na tsawon shekaru da danko mai karfi.

Soglo yana daya daga cikin shugabannin Afirka wanda yasa baki a lokacin Abacha aka kama Obasanjo kuma aka daure shi a 1995.

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya kai ziyara Zanzibar a ranar 1 ga watan Augusta don ya boye tafiyarsa zuwa jamhuriyar Benin, kamar yadda daya daga cikin majiyoyin ya shaida.
Yaje yi wa tsohon shugaban kasa Sogholo ta’aziyya ne bisa rasa matarsa da yayi a ‘yan kwanakin nan.

Boyayyar tafiya Obasanjo yayi

Wata majiyar kuma ta ce Obasanjo ya boye tafiyar ne:

Ya hadu da Patrice Talon. Dalilin haduwarsu shine don ya samu kyakkyawan masauki ga Sunday Igboho.
Yana bukatar Benin ta samar wa da Igboho masauki mai kyau kuma kada ta bari ya dawo Najeriya.
Tsohon shugaban kasar ya bukaci wasu daga cikin shugabannin kudu maso yamma da su sanya baki akan lamarin.

Kara karanta wannan

MURIC ta yi martani ga CAN: 2023 ba lokacin Shugaban kasa Kirista bane

Jami'an tsaro sun cafke Igboho a Cotonou

Jami’an tsaron Benin ne suka kama Igboho yayin da yake kokarin tserewa zuwa kasar Jamus.

Dama DSS sun bayyana a gidansa dake Oyo a ranar 1 ga watan Yuli har suka kashe mutane 2 kuma suka kama mabiyansa guda 12.

Yana hannun jami’an tsaro a Cotonou tun bayan kama shi da aka yi. Hadimin Obasanjo ya tabbatar da zuwansa jamhuriyar Benin.

TheCable ta gano yadda Obasanjo ya dawo Najeriya ta kasa ta iyakar Idiroko dake jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel