Zaben 2023: Wasu Sanatoci Biyu Zasu Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Zaben 2023: Wasu Sanatoci Biyu Zasu Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

  • Wasu sanatoci biyu da suka fito daga jihar Anambra zasu sauya sheka zuwa APC ba da jimawa ba
  • Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC a jihar, Basil Ejidike, shine ya bayyana haka
  • Yace zuwa yanzun APC ta yi wa mutum 500,000 rijistar zama cikakkun yan jam'iyya a jihar Anambra

Anambra - Jam'iyyar APC reshen jihar Anambra ta bayyana cewa ba da jimawa biyu daga cikin zaɓaɓɓun sanatocin a jihar zasu sauya sheka zuwa cikinta, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Wannna na zuwa ne bayan APC a jihar ta yi ikirarin yiwa mutum 500,000 rijistar zama yan jam'iyya a tsakanin watan Fabrairu zuwa Mayu, 2021.

Shugaban rikon kwarya na jihar, Chief Basil Ejidike, wanda ya yi tsokaci game da shirin sauya shekar, bai bayyana sunayen sanatocin ba.

Wasu Sanatoci Biyu Zasu Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC a Anambra
Zaben 2023: Wasu Sanatoci Biyu Zasu Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Su waye sanatoci uku dake wakiltar jihar?

A ranar Laraba da ta gabata tsohuwar sanata a jihar kuma mamba a kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Sanata Joy Emodi, ta koma APC.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam'iyyar APC, mambobin majalisar zartarwa duk sun yi murabus, sun koma PDP

Sanatocin dake kan kujerarsu a yanzun daga jihar Anambra sune, Sanata Ifeanyi Ubah, mai wakiltar mazabar Anambra ta kudu karkashin jam'iyyar YPP.

Sauran biyun sune Sanata Stella Oduah, mai wakiltar arewacin Anambra, da Sanata Uche Ekwunife, mai wakiltar Anambra ta tsakiya dukkansu yan jam'iyyar PDP.

Mun yi wa mutum 500,000 rijistar APC

Ejidike ya kara da cewa samun mutum 500,000 a jihar wani babban cigaba ne a jam'iyyar APC ta jihar.

A jawabinsa yace:

"Kafin gudanar da aikin rijistar APC muna da mambobi 200,000 a jihar, amma bayan aikin ina alfaharin sanar da cewa APC ta na da mambobi 500,000 a jihar Anambra."
"Wannan na nufin jam'iyyar ta kara samun karbuwa daga kadan zuwa sama da dubu 500,000, ina magana akan tabbacin mambobin APC na yanzun."

Waye dan takarar APC a zaɓen gwamna?

Dangane da zaɓen gwamnan jihar dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba, Ejidike yace har yanzun sanata Andy Uba shine ɗan takarar APC.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Cike da tashin hankali, Secondus ya koka kan yunkurin 'kwace' PDP

Ya kara cewa wanda aka tsayar ɗin gogaggen ɗan siyasa ne kuma ya taba takarar gwamna karkashin jam'iyyar PPA.

A wani labarin da muka kawo muku na daban kuma tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, IBB, ya bayyana babban dalilin da yasa sama da shekara 10 bai aure ba.

IBB yace a wancan lokacin bai sha wahala ba wajen samun matar da zai aura amma yanzun abun ba shi da sauki, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Allah ya yiwa matar Janar Ibrahim Badamasi Babangida rasuwa tun a shekarar 2009 kuma har zuwa yanzun bai sake wani auren ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel