Aure Babbar Sunnah: Matan Yanzun Basu Kaunar Aure Na, Tsohon Shugaban kasa IBB

Aure Babbar Sunnah: Matan Yanzun Basu Kaunar Aure Na, Tsohon Shugaban kasa IBB

  • Tsohon shugaban ƙasa a zamanin mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya fadi dalilin rashin aurensa
  • IBB ya bada amsa cikin raha da cewa matan yanzun basu kaunar aurensa shiyasa bai aure ba
  • Tsohon shugaban yace yin aure yanzun ba abune mai sauki ba kuma ya bada takaitaccen tarihin aurensa na fari

Minna, Niger - Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa mata basu kaunar fuskarsa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ya faɗi hakane yayin wata fira da kafar watsa labarai ta Arice TV a gidansa dake Minna, jihar Neja ranar Jumu'a.

A yayin firar tasa, tsohon shugaban ya yi tsokaci a kan wasu muhimman batutuwa da suka haɗa da tattalin arziki, siyasa, tsaro da kuma halin da ƙasa ke ciki.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

Ibrahim Badamasi Babangida
Aure Babbar Sunnah: Matan Yanzun Basu Kaunar Aure Na, Tsohon Shugaban kasa IBB Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Meyasa baka sake aure ba tun bayan rasuwar Maryam?

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokacin da aka kawo batun Maryam, marigayya matarsa, tsohon janar ɗin sojojin ya yi murumushi.

Da aka tambayeshi meyasa bai sake aure ba tun bayan mutuwar matarsa a 2009? cikin raha IBB ya amsa tambayar da cewa: "Matan yanzun basu kaunar fuskata."

Cikn hanzari ya kara bayani da cewa: "Ba abune mai sauki ba gaskiya, haka Allah ya so."

Takaitaccen tarihin auren IBB

Daga nan kuma sai ya fara bada takaitaccen tarihin yadda suka haɗu har ya auri marigayya matarsa, wadda suka haifi 'yaya huɗu.

IBB yace:

"A lokacin yakin basasa 1969 na samu raunuka sosai Ozokuli jihar Abia, daganan sai na dawo Lagos duk da ba abune mai sauki ba amma Allah ya taimake ni."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

"Janar Gawon ya yi aure a tsakanin wannan lokacin Afrilu ko Mayu, kuma shine jagorana kwamanda na. A lokacin na yi sha'awar yadda aurensu ya kasance."
"Ina gadon asibiti lokacin sai na tambayi kaina, da fa yanzun na mutu da bazan yi aure ba kenan kamar yadda shugabana yayi. Anan na yanke cewa da zaran na samu lafiya aure zan fara yi kafin komai. Kuma da taimakon Allah na warke."

Wane kalubale ka fuskanta wajen aure?

IBB ya kara da cewa a wancan lokacin nayi sa'a matar da zan aura da iyalanta duk sun amince da shi.

Tsohon shugaban yace:

"Nasanta sosai, ina yawan shiga gidansu a kan wasu dalilai saboda haka mun saba da yan uwanta mun zama kamar abokai."
"Lokacin da na nemi aurenta ban samu wani kalubale ba kowa ya amince. Bayan watanni kalilan aka ɗaura mana aure."

A wani labarin kuma Kotun Musulunci Ta Yi Fatali da Bukatar Sheikh Abduljabbar Kan Mukabala

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wata Fashewa Ta Halaka Rayukan Mutane, Ta Yi Mummunar Ɓarna a Wata Jiha

Bayan kammala mukabala tsakanin Abduljabbar da wasu malaman Kano, Shehin Malamin ya yi watsi da sakamakon da alkali ya bayyana

A cewar Abduljabbar ba'a masa adalci ba yayin wannan mukabala kuma babu isasshen lokaci.

Bisa wannan dalilin ne malamin ya garzaya gaban babar kotun Kano ya nemi da ayi watsi da shawarwarin da alkalin ya rubuta a rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel