Daga karshe, Hukumar Hizbah ta yi magana kan kayan da Zahra Bayero ta sanya

Daga karshe, Hukumar Hizbah ta yi magana kan kayan da Zahra Bayero ta sanya

  • Bayan kwanaki da bikin Bridal Shower, Hisbah ta mayar da martani ga jama'a
  • Kwamandan Hizbah ya ce laifi ne a addini a cigaba da yada hotunan a kafofin sada zumunta
  • Manyan malamai sun ce wannan abu da diyar Sarkin tayi bai dace ba

Kano - Hukumar Hisbah masu tabbatar da dabbaka koyarwan addinin Musulunci a jihar Kano ta yi magana daga karshe kan hotunan da sukayi yawo na diyar Sarkin Bichi, Zahra Nasir Bayero.

Zahra Nasir Bayero, budurwa ce ga 'dan gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, kuma ana shirin daura musu aure.

Zahra Bayero da kawayenta sun gudanar da bikin share faggen daurin aure 'Bridal Shower' kuma hotunan shagalin sun tayar da kura.

Jama'an Najeriya sun zargi hukumar Hisbah da son kai saboda ta ki magana kan lamarin don 'yayan masu fada a ji ne, sabanin abinda ake yiwa 'yayan talakawa a Kano idan sukayi irin haka.

Kara karanta wannan

Wannan fitsara ne: Malami ya yi tsokaci kan shigar da amaryar Yusuf Buhari tayi

Amma kwamandan Hisbah, Sheikh Harun Ibn Sina ya bayyanawa BBC cewa diyar Sarkin bata fi karfin doka ba kuma ya kamata ace ta nuna ita yar gidan manya ne idan tana neman albarka a aurenta.

Hakazalika Ibn Sina ya caccaki mutanen da ke yada hotunan da bidiyoyin Zahra Bayero inda yace laifi ne yada ire-iren hotunan.

Daga karshe, Hukumar Hizbah ta yi magana kan kayan da Zahra Bayero ta sanya
Daga karshe, Hukumar Hizbah ta yi magana kan kayan da Zahra Bayero ta sanya Hoto: zahrabayero
Asali: Instagram

Wannan fitsara ne: Malami ya yi tsokaci kan shigar da amaryar Yusuf Buhari tayi

Babban Malamin addinin Islama, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya yi tsokaci game da shigar da Zahra Bayero; amaryar Yusuf Buhari, yana mai nuna takaicin yadda 'ya'yan musulmai suka baci da shigar nuna tsiraici.

A makon nan wasu hotuna suka watsu a kafafen sada zumunta, wadanda ke nuna Zahra Bayero, budurwar da dan shugaban kasa Buhari zai aura sanye da wasu kaya masu nuna wane bangare na jikinta.

Wannan shiga da tayi ya jawo cece-kuce, yayin da mutane da dama suka nuna damuwarsu da cewa, wannan shiga bata yi dace da addinin Islama ba, kamar yadda budurwar take musulma.

Kara karanta wannan

Hotunan wankan amarya na Zahra Bayero sun bar baya da kura

Asali: Legit.ng

Online view pixel