Idan laifi Hadiza Bala Usman tayi ya zama wajibi a hukunta ta, Aisha Yesufu

Idan laifi Hadiza Bala Usman tayi ya zama wajibi a hukunta ta, Aisha Yesufu

  • Yan watanni bayan sabunta nadinta, shugaba Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman
  • Hadiza Bala ta rike kujerar shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwan Najeriya na tsawon shekaru 5
  • Ma'aikatar Sufuri, karkashi Rotimi Amaechi, na zarginta da aikata wasu laifuka

'Yar fafutuka da rajin kare hakkin jama'a, Aisha Yesufu, ta bayyana ra'ayinta game da dakatarwan da shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa tsohuwar shugabar hukumar NPA, Hadiza Bala Usman.

Aisha Yesufu a tattaunar da tayi Legit Hausa, ta bayyana cewa idan har ya tabbata ta tafka badakala toh kada a sassauta mata.

Ta kara da cewa babu ruwanta da kasancewar Hadiza Bala Usman mace 'yar uwarta, kawai a hukunta ta idan da gaske tayi laifi.

A cewarta, shugabanci hakki ne kuma duk wanda yayi ha'inci zai gamu da Allah ko shi waye.

Kara karanta wannan

Kisan Jos: Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari

Tace:

"Duk wanda aka sameshi da laifi, mace ne ko namiji, ko waye ya kamata a hukuntashi ko ita. Laifi babba, mutane na gani mukami abin wasa ne. Hakkin mutane na kanka."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan an tabbatar da zargin ya kamata a hukuntata. Idan ita kuma Hadizan ta san zargin da akayi mata ba gaskiya bane, ya kamata ta shigar da su kotu."

Me ake zargin Hadiza Bala da yi?

Ofishin mai binciken kudi a gwamnatin tarayya ya sake aika wasu takardu zuwa ga NPA, ya na zargin hukumar da rashin gaskiya wajen harka da kudi.

Jaridar Punch ta ce gwamnatin tarayya ta na zargin hukumar da yin aika-aika a shekarar 2018.

Daga cikin zargin da ke kan wuyan shugabanninn NPA akwai kin biyan hukumar FIRS harajin Naira biliyan 44.12 da yin facaka da Naira biliyan 88.23.

Kara karanta wannan

Ke ce addu'a ta da aka karba: Hanan Buhari da Muhammad Turad sun shekara 1 da aure

Binciken da gwamnatin ta yi ya nuna cewa NPA ta batar da Naira biliyan 409.17 da sunan sayen wasu kayan aiki, amma ba tare da an kawo takardun cinikin ba.

Har ila yau, Mista Aghughu ya na zargin NPA da rashin kokari wajen karbo bashin da ta ke bi.

Hukumar za kuma ta yi wa gwamnatin tarayya bayanin yadda aka kashe kusan Naira biliyan biyu a yarjejeniyar gidajen da ta shiga da Aso Savings & Loans Plc.

Badakalar NPA: Jam’iyyar PDP ta na so a hukunta Hadiza Bala Usman, a kai ta gidan yari

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira da a hukunta tsohuwar shugabar hukumar NPA da aka dakatar, Hajiya Hadiza Bala-Usman.

PDP ta na bukatar a hukunta Hadiza Bala-Usman ne a kan zargin da ake yi mata na cewa NPA ta karkatar da wasu Naira biliyan 165 a lokacin ta.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya aurar da diyarsa Hauwa ga dan Sarkin Azara

Premium Times ta ce PDP ta bayyana haka ne a wani jawabi da Kola Ologbondiyan ya fitar a garin Abuja, a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel