Bidiyon fusataccen dan Najeriya yana tallar ƙodarsa, yana tafe kan titi yana shela

Bidiyon fusataccen dan Najeriya yana tallar ƙodarsa, yana tafe kan titi yana shela

  • Wani fusataccen dan Najeriya ya bayyana a titin jihar Legas yana tallata kodarsa ga mai sha’awar siya
  • A bidiyon wanda shafin Naijaloaded suka wallafa a Instagram, an ga mutumin a gefen titi dauke da takarda yana tallar
  • Mutane da dama sun yi zargin tsabar talauci, kunci, takaici da matsin rayuwa ne suka janyo har mutumin ya aikata hakan

Legas - Bidiyon wani fusataccen dan Najeriya ya karade kafafen sada zumuntar zamani inda aka gan shi a tsakiyar titi yana shelar burinsa na sayar da kodarsa.

A bidiyon, an ga mutumin sanye da bakin tabarau a gefen titi dauke da takarda wacce ya rubuta “Ga koda mai kyau ta siyarwa”.

Bidiyon fusataccen dan Najeriya yana tallar ƙodarsa, yana tafe kan titi yana shela
Bidiyon fusataccen dan Najeriya yana tallar ƙodarsa, yana tafe kan titi yana shela. Hoto daga @naijaloadedotng
Asali: Instagram

Tuni mutane suka fara cece-kuce kowa yana tofa albarkacin bakinsa inda wasu suke cewa tsabar matsin rayuwa ne ya janyo masa hakan.

Wahala, kunci, takaici da talauci sukan saka mutum yayi abinda ba a saba gani ba musamman irin na wannan mutumin mai burin sayar da sassan jikinsa.

Kara karanta wannan

Yadda aka cafke matashi mai shekaru 16 da ke satar shanu da garkuwa da mutane

Ga dukkan alamu mutumin bai damu da maganar mutane ba

A bidiyon wanda Naijaloaded suka wallafa a shafinsu na Instagram an ga mutum sanye da bakaken kaya a bakin titi yana rike da wata takarda wacce yake tallata kodarsa.

Al’amarin da ya faru a jihar Legas. Legit.ng bata gano kwakkwaran dalilin da ya janyo har mutumin yayi wannan abu ba har a lokacin rubuta wannan rahoton.

Ga bidiyon:

Bayan sanar da shirin rabuwa, Bill Gates da Melinda sun tsinke igiyoyin aurensu

Auren mashahurin mai kudin nan na duniya Bill Gates da matarsa Melinda French Gates ya rabu kamar yadda alkali ya amince da rabuwar tasu, theCable ta wallafa.

Dama sun gabatar da takardar amincewa da rabuwar aurensu mai shekaru 27 tun 3 ga watan Mayu zuwa babbar kotu ta King County dake Washington kuma an tabbatar da rabuwar tasu a ranar Litinin. Bill da Melinda sun jima suna yada rabuwar aurensu kuma sun amince da yadda zasu raba auren.

Kara karanta wannan

Hotunan wankan amarya na Zahra Bayero sun bar baya da kura

Sai dai kamar yadda Reuters suka tabbatar, babu wani dogon bayani akan rabuwar auren sannan babu batun raba kudade, kadarori ko wasu dukiya dake tsakaninsu a rabuwar auren.

Rahoton kotu ya bayyana cewa babu wanda zai canja sunansa cikinsu ko kuma ya samu wani tallafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel