Yunkurin korar Secondus da sauran Shugabannin PDP ya sa Gwamnoni sun rabu zuwa gida uku

Yunkurin korar Secondus da sauran Shugabannin PDP ya sa Gwamnoni sun rabu zuwa gida uku

  • Makomar majalisar NWC da ke karkashin Prince Uche Secondus ya raba PDP
  • Wasu Gwamnonin jam’iyyar PDP ba su tare da shugabansu, Prince Secondus
  • Mafi yawan Gwamnonin adawan suna goyon bayan Secondus da Majalisarsa

Abuja - Gwamnonin da ke karkashin jam’iyyar adawa ta PDP sun raba jiha sosai a game da makomar shugabansu na kasa, Prince Uche Secondus.

Wa’adin ‘yan majalisar aiwatarwa ta jam’iyyar PDP watau NWC zai kare ne a watan Disamba, amma wasu gwamnoni suna huro masu wuta tun yanzu.

The Nation ta ce bangaren gwamna Nyesom Wike suna so a sauke shugabannin jam’iyyar daga kujerunsu kafin su cinye lokacinsu a karshen shekarar nan.

Rahoton ya ce daga cikin gwamnoni 14 da PDP ta ke da su, takwas suna goyon bayan Prince Uche Secondus da ‘yan majalisar ta sa a rigimar gidan da ake yi.

Haka zalika akwai gwamnoni uku da ba su goyon bayan shugaban jam’iyyar ya cigaba da zama a kujerarsa. Sauran gwamnoni ukun suna kallon ikon Allah.

Kara karanta wannan

Osinbajo su na kokarin fitar da APC daga tirka-tirkar shari’ar da za a iya shiga nan gaba

“Rikicin cikin gidan ya raba kan jam’iyya. Gwamnoninta ba su tare duk da taron da aka yi a watan jiya a Bauchi, inda aka ga kamar gwamnonin sun sasanta.”

Shugabannin PDP
Magoya bayan PDP Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Yadda kan gwamnoni ya rabu?

Gwamnonin da suke adawa da majalisar Secondus sun hada da – Nyesom Wike (Ribass), Seyi Makinde (Oyo) da kuma Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa).

A bangaren nan akwai tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu wanda yake rikici da gwamnatin Ugwuanyi kan zaben 2023.

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto), Samuel Ortom (Benue) da Mai girma gwamna Emmanuel Udom (Akwa Ibom) ba su zabi bangare a rigimar ba.

Sauran gwamnonin adawar ba su yaki da shugaban PDP, suna goyon bayan ya cigaba da rike jam’iyyar. Daga ciki akwai Sanata Douye Diri da Darius Ishaku.

Ragowar sun hada da; Ifeanyi Ugwuanyi, Okezie Ikpeazu, Bala Mohammed, Ifeanyi Okowa, Godwin Obaseki, da mataimakin gwamnan Zamfara, Mahadi Aliyu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: PDP ta saki bidiyo, ta yanke muhimmiyar shawara

Rikicin cikin gidan PDP

An ji cewa lamarin ya kare cabe wa jam'iyyar adawar bayan Diran Odeyemi; Ahmed Bello; Hadizat Umoru; da Divine Amina Arong sun ajiye mukamansu a NWC.

Haka zalika Hassan Yakubu da Irona Alphonsus sun yi murabus, suna sukar salon jagorancin Secondus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel