Osinbajo su na kokarin fitar da APC daga tirka-tirkar shari’ar da za a iya shiga nan gaba

Osinbajo su na kokarin fitar da APC daga tirka-tirkar shari’ar da za a iya shiga nan gaba

  • Farfesa Yemi Osinbajo ya na kokarin ceto APC daga kangin shari’a da ta shiga
  • Alkalai sun haramta wa Gwamna Mai Mala Buni rike kujerar Shugaban APC
  • Mataimakin Shugaban kasar ya tuntubi manyan am’iyya domin samun mafita

Abuja - Mai girma mataimakain shugaban kasa, Yemi Osinbajo da gwamnonin jihohin APC suna nema wa jam’iyyarsu mafita kan halin da aka shiga.

An hada Farfesa Osinbajo da aiki

The Nation ta fahimci cewa Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnoni suna yunkurin yadda za a samu maslaha bayan hukuncin kotun koli a kan zaben Ondo.

Jaridar ta ce har yanzu ba a san matakin da mataimakain shugaban kasan da gwamnonin za su dauka ba, amma ana kokarin guje wa matsalar shari’a.

Wasu daga cikin manyan APC suna tare da karamin Ministan kwadago, Festus Keyamo SAN da tsohon mai ba jam’iyya shawara, Babatunde Ogala SAN.

Wasu kuma suna ganin babu dalilin tada hankali a game da hukuncin da wasu Alkalan kotu suka zartar.

Kara karanta wannan

An tono wasikar da Marigayi Jafar Adam ya rubutowa Diyarsa shekaru 20 da suka wuce

Majiyar ta ce ba a iya tsaida zaben shugabannin mazabu a makon da ya wuce ba ne saboda sabanin da aka samu tsakanin Darfesa Osinbajo da Mala Buni.

Ana sa ran cewa mataimakin shugaban kasar a matsayinsa na Farfesa, masanin shari’a kuma tsohon lauyan gwamnati, ya iya nema wa jam’iyyar mafita.

Osinbajo
Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo Hoto; punchng.com
Asali: UGC

Halin da ake ciki

“Mataimakin shugaban kasa ya na kan ra’ayin cewa hukuncin da Alkalan kotun koli suka yi babbar matsala ce a fuskar shari’a, wanda ya kamata a guje mata.”
“Ya (Osinbajo) na so a tabbatar da cewa an sa jam’iyya a rai, duk masu ruwa da tsaki su samu mafita domin mutanen Najeriya su kara amanna da tafiyar APC.”
“Farfesa Osinbajo ya na ta tuntubar gwamnoni da shugabannin jam’iyya a kan abin da ya dace ayi domin a ceci APC daga tarkon da za ta iya auka wa a gaba.”

Hukuncin kotun koli

Tsoron da ake yi shi ne kotu za ta iya ruguza duk matakin da APC ta dauka a karkashin jagaorancin Mai Mala Buni saboda yana kan kujerar gwamna.

Kara karanta wannan

A yanzu kam manufar mu ita ce sama wa 'yan Najeriya aiki, in ji Gwamnatin Buhari

Alkalan kotun koli uku; Mary Odili, Ejembi Eko da Mohammed Saulawa duk sun bayyana cewa doka ba ta ba gwamna dama ya rike shugabancin jam’iyya ba.

Da farko an ji yadda Gwamna Mala Buni da Abubakar Malami SAN suka yi fatali da shawarar Yemi Osinbajo a kan batun zaben shugabannin APC da aka fara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel