Shugaban Nijar ya yaba da aikin gwamnan Borno Zulum, ya bashi lambar girmamawa

Shugaban Nijar ya yaba da aikin gwamnan Borno Zulum, ya bashi lambar girmamawa

  • Gwamnan jihar Borno ya karbi lambar yabo mai girma a kasar Nijar saboda jajircewarsa
  • Gwamnan ya je kasar ne domin karbar lambar girmamawa, wanda shine na farko da ya fara karba
  • Ya samu rakiyar wasu jiga-jigan siyasar jihar ta Borno a yayin karbar wannan babbar girmamawa

Shugaban kasar Nijar, Mohammed Bazoum ya bai wa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, lambar girmamawa ta kasa mai suna "de Grand Officer dans I`Ordre" sakamakon irin rawar da ya ke takawa a yaki da matsalolin rashin tsaro.

Shugaba Bazoum ya ce girmama Zulum ya zama masa wajibi lidan aka yi a'akari da namijin kokarin da Zulum ke nunawa a yakar Boko Haram, damuwar da yake nunawa kan 'yan gudun hijira da kokarin sake tsugunar da su a yankunansu da yaki ya lalata.

An gudanar da bikin karrama Zulum ne a birnin Zinder, a wani bangare na bikin ranar yanci da Nijar ke gudanawar a ranar Talata 3 ga watan Agustan 2021, BBC ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Siyasa: Atiku ya fara kyakkyawan shirin kamfe don karbe mulkin Najeriya a 2023

Shugaban kasar Nijar ya yaba da aikin gwamnan Borno Zulum, ya bashi lambar yabo
Shugaban kasar Nijar tare da Gwamna Zulum | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Wannan shi ne karo na farko da wani shugaba a Nijar ke bai wa gwamna a Najeriya irin wannan lambar girmamawa.

Zulum ya je Nijar din ne da rakiyar Sanata kashim Shettima da dan majalisa Mohammed Ali Ndume da kakakin majalisar jihar Borno Mohammed Tahir Monguno da wasu kwamishinoninsa.

Gwamna Zulum ya zabi mazajen mafarauta 1000 domin kare manoma daga Boko Haram

Babagana Umara Zulum, gwamnan jihar Borno, a ranar Alhamis, ya rantsar da mafarauta 1,000 domin yaki da Boko Haram, The Cable ta ruwaito.

Aikin mafarautan shi ne kare manoman da ke noma albarkatun gona a wajen garin Jere, babban birnin Maiduguri, kananan hukumomin Konduga da Mafa na jihar.

An rantsar da mafarautan ne makonni kadan bayan jami'an tsaro na farin kaya (DSS) da sojojin sun gama tantance su.

Gwamnan ya ce:

"Mafarautanmu na cikin gida sun zama wani bangare na labarin nasararmu saboda rawar da suke takawa a kokarin magance matsalolin tsaro da muke fuskanta a jihar.

Kara karanta wannan

Rudani a Kano bayan majalisar jiha ta gayyaci shugaban alkalai kan shari'ar Rimingado

“Wannan ya sa muka tsunduma neman karin mafarauta don taimaka wa sojojinmu a kokarin da suke yi wanda ba za a iya musantawa ba kuma abin yabo na kokarin kawo karshen tayar da kayar baya.”

Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi

A wani labarin, Gwamnatin Jihar Sokoto ta raba Naira miliyan 21.7 ga gundumomi 87 don sayan shanun sallah ga marayu, Daily Trust ta ruwaito.

An ba kowace daga cikin gundumomin N200,000 na sayen saniya da kuma N20,000 don jigilar ta.

A yayin kaddamar da bayarwar, Sultan na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar Said, ya gode wa gwamnatin jihar bisa ci gaba da wannan aikin duk da raguwar albarkatun ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel