Bidiyon fitaccen Faston Najeriya yana karanta ayoyin Alkur'ani mai girma

Bidiyon fitaccen Faston Najeriya yana karanta ayoyin Alkur'ani mai girma

  • Tunde Bakare, babban faston Najeriya da ake girmamawa ya ba da labari mai ban sha'awa na yadda ya zama Kirista
  • Da yake karanto wasu ayoyin Alkur’ani, malamin kiristan ya ce ya fito ne daga gidan Musulunci mai karfi a jihar Ogun
  • Fitaccen fasto ya ce zamowarsa Kirista nufin Allah ne, yana mai cewa bai zama Kirista saboda wata cuta ba

Lagos, Nigeria - Fasto Tunde Bakare, shugaban cocin Layyer Rain Assembly, ya ba mutane da yawa mamaki yayin da aka gano shi yana karanta wasu ayoyin Alkur'ani a lokacin da yake hira da BBC Yoruba.

A cikin hirar da aka buga a ranar Talata, 3 ga watan Agusta, fasto din da ake girmamawa ya bayyana cewa ya fito ne daga gidan Musulunci mai karfi.

Bidiyon fitaccen Faston Najeriya yana karanta ayoyin Alkur'ani mai girma
Fasto Tunde Bakare ya bayyana cewa iyayensa Musulmai ne Hoto: Pastor Tunde Bakare
Asali: Facebook

A cewar Fasto Bakare, kakansa shine limamin Sodeke na farko a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Ya kara da cewa mahaifinsa Cif Sani Adekunle Bakare Musulmi ne mai ibada.

Kara karanta wannan

Allah Zai Wanke Abba Kyari, Hassada Wasu Ƴan Sanda Ke Masa: Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin ‘Brekete Family’

Fasto Bakare ya ce ya fara karatun addinin Musulunci da na Larabci tun yana dan shekara hudu kuma ya yi walimah kammala karatu a 1967.

Malamin ya ce yana iya karatun Alqur'ani, littafi mai tsarki tun daga farko har zuwa karshe, yana mai cewa Allah ne ya nufe shi da zama Kirista.

Yadda na zama Kirista

Lokacin da yake da shekaru 20, Fasto Bakare ya ce wani abokinsa mai suna Ganiu, wanda shi ma Musulmi ne ya zama Kirista, ya so ya yi taro a coci kuma ya gayyace shi ya rufe taron a matsayin mai daukar hoto.

Ya ce a wurin taron ne wahayi da Allah ya nuna masa yana dan shekara 10 a shekarar 1964 ya fara dawowa idanunsa a cocin.

Fasto Bakare ya bayyana cewa sakon mai hudubar ya birge shi, inda ya bayyana cewa bai zama Kirista saboda rashin lafiya ko wani abu daban ba.

Ya kara da cewa ba tare da bata lokaci ba ya bayyana wa yan uwansa cewa ya zama Kirista kuma cewa yana zuwa coci ne a sirrince don karin sani a kan addinin.

Kara karanta wannan

Babban Limamin kasa, Maqary ya yi barazanar kai Shehin da yi masa kazafi gaban Alkali

Na ayyana wa ahlina addinin Kirista a 1974

Fasto Bakare ya ce a ranar 14 ga Oktoba, 1974, ya yanke shawarar gaya wa danginsa cewa yanzu shi tubabbe ne kuma ba zai sake yin addinin Islama ba.

A cewarsa, daga baya an kore shi daga gidan. Cocinsa ne ya kawo masa agaji ta hanyar ba shi masauki.

Fasto Bakare ya ce da yawa daga cikin danginsa, ciki har da mahaifiyarsa da ta je Makka don yin aikin Hajji, daga baya sun zama Kiristoci.

Ba Zan Taɓa Mantawa da Fasto Tunde Bakare ba, El-Rufa'i Ya Faɗi Alƙarsa da Faston Coci

A wani labari na daban, gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya bayyana alaƙar dake tsakninsa da Fasto Tunde Bakare na cocin addinin kirista, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

El-Rufa'i, yace Fasto Bakare shine ya gabatar da shi ga shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, da tsohuwar jam'iyyarsa wato CPC.

Kara karanta wannan

An daure shugaban matasan PDP a gidan yari saboda ya zagi Buhari, SGF a Facebook

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin wata fira da yayi da sashin BBC na yaren Fijin, wanda ya gudana a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel