MURIC ta yi martani ga CAN: 2023 ba lokacin Shugaban kasa Kirista bane

MURIC ta yi martani ga CAN: 2023 ba lokacin Shugaban kasa Kirista bane

  • Ga dukkan alamu fafatawa da ake yi game da shugabancin 2023 ya ɗauki salon addini tsakanin MURIC da CAN
  • Kungiyar Musuluncin ta mayar da martani kan sanarwar baya bayan nan da Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta fitar
  • Kungiyar Kiristocin a baya ta dage kan cewa dan kirista ne ya kamata ya zama shugaban Najeriya na gaba

Lagos - Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi (MURIC), ta mayar da martani kan sanarwar da kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta fitar kwanan nan inda ta yi kira ga shugaban kasa dan Kirista a 2023.

MURIC ta ce ita bata adawa da samar da shugaban Najeriya kirista, amma cewa dole ne CAN ta jira zagayen ta, jaridar Daily Post ta ruwaito.

MURIC ta yi martani ga CAN: 2023 ba lokacin Shugaban kasa Kirista bane
Farfesa Akintola ya ce dole ne CAN ta jira bayan 2023 kafin ta samar da shugaban kasa Hoto: MURIC
Asali: Facebook

Darakta kuma wanda ya kafa MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana matsayin kungiyar a ranar Litinin, 2 ga Agusta a cikin wata sanarwa.

Sashin bayanin ya zo kamar haka:

Kara karanta wannan

Hushpuppi: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya gaya wa Buhari abin da ya kamata ya yi na mika Abba Kyari

“Cif Mathew Aremu Olusegun Obasanjo, Kirista, ya kwashe shekaru takwas yana shugabantar kasa. Dr. Goodluck Ebele Jonathan shima ya kwashe shekaru biyar. Wannan ya kawo jimlar da shugabannin Kiristoci suka kashe a Aso Rock zuwa shekaru goma sha uku.
"Musulmai za su ragu a shekaru biyu ko hudu idan Kirista ya zama shugaban kasa a 2023. Abin da ya fi dacewa shi ne a bar wani Musulmi ya yi wa'adi daya kacal daga 2023 zuwa 2027."

Kungiyar ta shawarci CAN da ta jira lokacin ta sannan ta kara da cewa ya kamata kungiyar Kiristocin ta daina rura wuta a yanayin siyasa da bukatu.

Ba zamu yarda Bayarabe wanda ba Musulmi ba ya zama shugaban kasa, MURIC

A wani labarin, kungiyar kare hakkin Musulmai watau MURIC ta bayyana cewa ba zai yiwu a baiwa wani dan kabilan Yoruba tikitin takarar shugaban kasa ba idan ba Musulmi bane.

A jawabin da shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya sake ranar Litinin, ya bayyana cewa tsohon shugaba Obasanjo na kokarin shigo da shugaban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina, cikin takarar kujeran shugaba a 2023.

Kara karanta wannan

2023: ‘Yan Najeriya na Allah-Allah PDP ta dawo, In ji Atiku yayin da ya hadu da Wike don yin sulhu

A cewarsa, kokarin sanya Adesina wanda Bayarabe Kirista ne cikin takaran rashin adalci ne da daidaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel