'Yar autan Malam Ibrahim Shekarau ta rasu, an birne ta a Dubai
- Allah ya yi wa yar autan Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Kano rasuwa
- Jinjinran yar watanni biyar ta rasu ne bayan an kwatar da ita a asibiti a Dubai
- Dr Sule Yau, hadimin Sanata Shekaru ya ce an birne yarinyar a can kasar ta Dubai
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a yanzu sanata mai wakiltan Kano Central a Majalisar Dattawar Nigeria, ya rasa yarsa mai watanni biyar a ranar Litinin a Dubai, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Sanarwa da mashawarcin Shekarau kan watsa labarai, Dr Sule Yau, ya fitar a ranar Litinina Kano ta ce a can kasar na Dubai da yarinyar ke jinya a asibiti aka birne ta.

Asali: Twitter
Sanarwar ta Dr Sule ta ce:
"Cikin jimami, muna sanar da rasuwar yar autar mai girma, Sanata Ibrahim Shekarau, jinjira yar watanni biyar da ta rasu a yau. An riga an birne ta a kasar Dubai inda aka kwantar da ita a asibiti."
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng