Sabon Bincike: Yadda Hushpuppi ya aika wa Abba Kyari miliyoyi na wata harkalla

Sabon Bincike: Yadda Hushpuppi ya aika wa Abba Kyari miliyoyi na wata harkalla

Ana ci gaba da cece-kuce game da dakatar da Abba Kyari biyo bayan zargin da FBI ta yi akansa na hada hannu da Hushpuppi wajen saukaka wata damfara da aka aikata kan wani dan kasuwa. Rahoto daga kasar Amurka ya bayyana dalla-dalla yadda lamarin yake.

Califonia, Amurka - Awanni bayan da hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta dakatar da DCP Abba Kyari bisa shawarin Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Baba, Cibiyar Binciken Manyan Laifuka TA FBI Ta bayyana sabbin bayanai game da Abba Kyari.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, FBI ta yi zargin Abass Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi, ya bai wa Abba Kyari N8m ko $20,600, don kamawa da tsare wani abokin harkallarsa mai suna Kelly Vincent.

Legit.ng ta tattaro cewa jaridar ta ce batun na cikin takardar da Kotun Amurka ta bayar na gundumar tsakiyar California mai dauke da kwanan wata 12 ga Fabrairu, 2021.

Kara karanta wannan

Kwamitin jami'an tsaro mai mutum 4 da zai binciki Abba Kyari ya fara aiki bayan dakatarwa

Sabon Bincike: Yadda Hushpuppi ya aika wa Abba Kyari miliyoyi na wata harkalla
Huspuppi da Abba Kyari | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Takardar ta yi zargin cewa Hushpuppi ya ba Kyari kwangila bayan da Chibuzo ya yi barazanar fallasa wani zamba na dala miliyan 1.1 da suka aikata a kan wani dan kasuwa na kasar Qatar.

A cewar rahoton, shafi na 59, sakin layi na 145 na takardar ya bayyana cewa Kyari ya bayar da bayanan asusu na wani asusun bankin Najeriya mai dauke da sunan da ba nashi ba.

An bayyana cewa jami'in FBI na musamman, Andrew John Innocenti, ya yi wannan zargin ne a cikin 'kararrakin laifuka ta wayar tarho ko wasu hanyoyin dogaro na fasaha' da aka shigar a gaban kotun Amurka na gundumar tsakiyar California.

Kyari da Hushpuppi sun tattauna ta manhajar WhatsApp

Takardar, a cewar jaridar Punch, ta yi bayani dalla-dalla na abubuwan da suka haifar da zargin cewa Hushpuppi ya biya Kyari kudi, ya kara da cewa Hushpuppi ya aika wa Kyari sako a ranar 16 ga Janairu, 2020, ta manhajar WhatsApp.

Kara karanta wannan

Zargin Abba Kyari: An nada kwamitin mutum 4 da zasu binciki Kyari cikin makon nan

Takardar ta ce:

“A ranar 16 ga Janairun 2020, Abbas ya aika wa Kyari sako ta WhatsApp, sannan ya kira shi sau biyar da wata lambar waya (+2348060733588) da aka aje a matsayin 'Abba Kyari'.
"Bayanan kira sun nuna cewa an amsa kira uku na karshe. kuma tsawon kiran ya dauki fiye da mintuna biyu.
"Jim kadan bayan haka, Abbas ya karbi sako daga Kyari, yana tabbatar da 'Za mu dauke shi a yau ko gobe.' Abbas ya rubuta, 'Zan kula da tawagar bayan sun dauke shi.' Kyari ya tabbatar da 'Yes ooo'"

Ta kuma kara da cewa dangane da tattaunawar da aka bayyana a sakin layi na 143 zuwa 145, Abbas ya yi niyyar biyan jami'an 'yan sandan Najeriya da suka yi aikin kama Chibuzo.

Takardar ta yi zargin:

“Wannan ba shine kadai lokacin da Abbas ya shirya biyan kudi ga Kyari ba.
"A ranar 20 ga Mayu, 2020, Abbas ya aika da shaidar biya ga Kyari na harkalloli guda biyu daga asusun bankunan Najeriya na mutumin da Abbas ya sani a U.A.E wanda shi ma 'yan sandan Dubai a ranar 9 ga Yuni, 2020 sun kame shi - zuwa asusun bankin Najeriya na wani mutum a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

Adadin kudaden da aka samu na harkallar sun kai Naira miliyan 8 na Najeriya, wanda kusan $20,600 ne bisa bayanan canjin kudi na hannun jama'a."

Takardar FBI ta lura cewa:

"A kokarin fahimtar Abbas, a ranar 18 ga Janairu, 2020, Chibuzo ya ba da labarin duk taimakon da ya bayar a cikin shirin damfarar dan kasuwa da aka damfara, gami da kirkirar takaddar "ikon lauya", kirkirar labari don gaya wa dan kasuwan, da kuma a saukake kirkirar lambar “banki ta waya” da gidan yanar gizon Wells Fargo na bogi.
“A ranar 20 ga Janairu, 2020, Kyari ya aika wa Abbas wani sako, wanda ke tantance bayanan Chibuzo, tare da hotonsa. A cikin hirar tasu, nan da nan, Abbas ya tabbatar da cewa, '' shi ne yallabai."

Zargin Abba Kyari: An nada kwamitin mutum 4 da zasu binciki Kyari cikin makon nan

A wani labarin, Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda (DCP), na iya bayyana a gaban kwamiti na musamman da ke binciken zarginsa da hannu a zambar intanet a wannan makon, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An dakatar da Abba Kyari daga aiki kan zargin hada kai da Hushpuppi, an fara bincikarsa

Ku tuna cewa hukumar kula da ayyukan 'yan sanda (PSC) a ranar Lahadi, 1 ga watan Agusta, ta dakatar da Kyari daga aiki kamar yadda sufeto janar na 'yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba, ya shawarta a ranar Asabar, 31 ga watan Yuli.

PSC ta bayyana cewa za a dakatar da Kyari har sai an kammala bincike kan tuhumar da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta yi, in ji jaridar The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel