Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyukan Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 18

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyukan Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 18

  • Yan bindiga sun mamayi ƙauyuka biyar a yankin karamar hukumar Kauru dake jihar Kaduna
  • Maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi inda suka hallaka mutane aƙalla 18 yayin harin
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa bayan hasarar rayuwa maharan sun lalata dukiya ta makudan miliyoyi

Kaduna:- Aƙalla mutum 18 ne suka rasa rayukansu ciki har da ɗan sanda a wani harin da yan ta'adda suka kai kauyuka biyar dake yankin Chawai, karamar hukumar Kauru, jihar Kaduna.

Ƙauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da Kigom, Kikoba, Kishisho da kuma Unguwan Magaji.

Da yake magana da jaridar dailytrust, wani mazaunin ɗaya daga cikin ƙauyukan da lamarin ya shafa, yace yan bindiga sun kai hari kauyukan su inda suka buɗe wuta kan duk wani abu da suka gani.

Wasu yan bindiga sun kai hari kauyukan Kaduna
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyukan Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 18 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mutum nawa aka kashe a kowane kauye?

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutum shida a ƙauyen Unguwan Magaji, shida a Kikoba, ɗaya a Kigom da kuma biyar a Kishisho.

Kara karanta wannan

Zamu Tona Asirin Yan Ta'addan Cikin Mu, Shugabannin Fulani Sun Yi Alkawari

Mazaunin ɗaya daga cikin kauyen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace:

"Yan bindigan sun lalata kadarori na miliyoyin kudi wanda ya hada har da gonakin da mutane ke nomawa yankunan."

Sai dai har zuwa yanzun kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, bai ɗaga wayar da aka masa ba kuma bai turo amsar sakonnin da ake tura masa ba domin jin ta bakinsu.

Fulani sun yi alƙawarin fallasa yan ta'adda

A wani labarin kuma Zamu Tona Asirin Yan Ta'addan Cikin Mu, Shugabannin Fulani Sun Yi Alakawari

Shugabannin Fulani makiyaya na jihar Taraba sun yi alƙawarin bankaɗo bara gurbin cikin su a cikin watanni biyar, kamar yadda Pm News ta ruwaito.

Fulanin sun ɗauki wannan alkawarin ne a wani jawabi da suka fitar bayan sun halarci wani taro a fadar mai martaba Sarkin Muri dake Jalingo,.

Asali: Legit.ng

Online view pixel