Gwamnatin Buhari ta gargadi matasan Najeriya cewa ya kamata su rage son kudi

Gwamnatin Buhari ta gargadi matasan Najeriya cewa ya kamata su rage son kudi

  • Gwamnatin tarayya ta gargadi matasa kan yawaitar fita daga Najeriya da sunan neman aiki
  • Ta ce, ya kamata 'yan Najeriya su gane cewa, ba komai ake yi don kudi ba, kar su jefa kansu ga hadari
  • Hakazalika, gwamnati ta ce a rage son kudi, kuma gwamnati na aiki tukuru don gyara tattalin arziki

Gwamnatin tarayya ta gargadi matasan da ke neman guraben aikin yi a kasashen waje da su yi taka tsantsan, don kada su fada hannun masu fataucin mutane, The Cable ta ruwaito.

Memunat Idu-Lah, daraktar hulda da al'adu na kasa da kasa a ma'aikatar yada labarai da al'adu, ta bayyana haka ne a wata hira da NAN a ranar Lahadi, 1 ga watan Agusta.

Idu-Lah, wacce ta shawarci matasa da su nemi aiki a cikin kasar nan, ta ce akwai shirye-shiryen karfafawa daban-daban na gwamnatin tarayya wadanda za su iya ba matasa damar samun fa'ida.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

Gwamnatin Buhari ta shawarci matasan Najeriya da su rage son kudi
Matasan Najeriya | Hoto: businesspost.ng
Asali: UGC

A kalamanta:

“Ya kamata matasan mu su kalli cikin gida su zama masu fasaha. Kowa yana da tasa fasaha ko wani abu. Kowane mutum yana da baiwar da aka haife shi a wannan duniyar.
“Ina ganin ya kamata mu hana matasa fita. Idan suna bukatar tallafi, akwai wasu hukumomin gwamnati wadanda aka dora wa alhakin samar da shirye-shiryen karfafawa da yawa.
“Wadannan hukumomin za su iya tallafa wa matasa su koyi wani abu kuma su kasance masu fa’ida, maimakon kallonsu suna guduwa. Kada mu yi tunanin fita. Ya kamata mu yi kokari mu kalli cikin gida mu yi imani da shirye-shiryen gwamnati.
“Hukumar kananan sana'o'i (SMEDAN) tana nan, da kuma shirye-shirye da yawa da gwamnati ta yi don taimakawa matasa - don karfafa su.”

Kada neman kudi ya kai ku ga shiga hannun masu fataucin mutane

Daraktar ta kuma gargadi matasa da su guji fadawa hannun safarar mutane a kokarinsu na neman aiki a kasashen waje, a cewar The Street Journal.

Kara karanta wannan

Duka Ma’aikatan fadar Shugaban kasa sun dauki rantsuwar hana sirri fita daga Aso Rock

A cewarta:

“Mutanen da za su zo su dauke su ba za su fada musu gaskiya ba. Sai bayan lokacin da aka dauke yara suka fice daga kauyensu, suna tare da masu fataucinsu nan ne suke gane gaskiya, a wannan lokacin kuwa sun makara kuma ba za su iya dawowa ba."

Ta kuma jawo hankulan matasa 'yan Najeriya cewa, ba komai ne dole sai da kudi ba, tana mai shawartar cewa, ya kamata 'yan Najeriya su zauna a gida domin habaka samar da kayayyakin gida da ya kamata 'yan kasa su sarrafa.

Ta kuma kara da cewa, gwamnatin shugaba Buhari na iya kokarinta don ganin an farfado da tattalin arzikin kasa da kuma tallafawa matasa.

Gwamnatin Buhari ta gargadi mazauna waje kan daukar nauyin masu rikita Najeriya

A wani labarin, Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya gargadi kungiyar 'yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDO) kan daukar nauyin kungiyoyin 'yan aware.

Kara karanta wannan

Rahoto: Manyan shari'u 5 da aka fi damuwa dasu saboda muhimmancinsu amma aka mance su

Lai Mohammed ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar NIDO, reshen Burtaniya ta kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata, 27 ga watan Yuli.

Ministan ya ce abin takaici ne yadda kungiyoyin 'yan aware da ke fafutuka a duniya kuma suke amfani da wasu mambobin NIDO wajen yada labaran karya game da kasa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel