An daure shugaban matasan PDP a gidan yari saboda ya zagi Buhari, SGF a Facebook

An daure shugaban matasan PDP a gidan yari saboda ya zagi Buhari, SGF a Facebook

  • Ikama Kato ya caccaki Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a wani bidiyo
  • Hakan ya sa PDP ta dakatar da shugaban matasan ta na karamar hukumar Hong
  • Bayan haka an kai Kato gaban wani Alkali, inda aka bukaci a tsare shi a kurkuku

Adamawa - Shugaban matasa na jam’iyyar PDP a karamar hukumar Hong, jihar Adamawa, da aka dakatar, Ikama Kato, ya na cigaba da ganin ha’ula’i.

Punch ta fitar da rahoto a safiyar yau, Litinin, 2 ga watan Agusta, 2021, cewa an tsare Mista Ikama Kato a gidan yari ne saboda zargin ya zagi shugabanni.

Ikama Kato wanda ya fito daga yanki guda da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya je shafinsa na Facebook ne ya na koka wa da halin tsaro.

Jagoran matasan PDP ya yi baram-barama a bidiyo

Kato ya soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a shafin sada zumunta bayan wasu ‘yan bindiga da ake zargin Boko Haram ne sun kai masu hari.

Kara karanta wannan

Hushpuppi: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya gaya wa Buhari abin da ya kamata ya yi na mika Abba Kyari

A wani bidiyo da ya ke ta yawo, jaridar ta ce Kato ya yi kaca-kaca da Boss Mustapha da Muhammadu Buhari, ya ce sun gaza tsare ran al’umma.

Jagoran matasan jam’iyyar hamayyar ya bayyana Boss a matsayin wanda ya gaza, ya kuma ba su kunya.

Buhari da SGF
Buhari da SGF Boss Mustapha Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Har ila yau, Mista Kato bai tsaya nan ba, ya kira Mai girma shugaban kasa da sakataren gwamnatin tarayyan da ‘mutane marasa amfanin komai’.

Da samun wannan bidiyo, sai PDP mai mulki a jihar Adamawa ta reshen karamar hukumar Hong, ta dakatar da Kato saboda amfani da kalmomi marasa dadi.

An kai karar Ikama Kato a gaban kotun majistare

Daga baya, Ikama Kato ya fito ya yi jawabi a wani sabon bidiyo a cikin da-na-sani, ya nemi afuwa. Amma duk da haka, aka kai karar shi a wani kotu a Yola.

Alkalin kotun majistaren da ke garin Yola, Dimas Gwama, ya karbi karar da aka shigar, ya bukaci a tsare wanda ake zargi a cikin gidan yari zuwa yau Litinin.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

Dazu ne tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, watau INEC ya caccaki manyan jam'iyyun Najeriya na APC da PDP, ya ce duk tafiyarsu daya.

Farfesa Attahiru Jega ya gargadi mutanen Najeriya a kan sake zaban 'yan siyasar da suka fito daga jam'iyyun nan, a cewarsa duk jirgi daya ne ya dauko su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel