Hushpuppi: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya gaya wa Buhari abin da ya kamata ya yi na mika Abba Kyari

Hushpuppi: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya gaya wa Buhari abin da ya kamata ya yi na mika Abba Kyari

  • Kingsley Moghalu, tsohon dan takarar shugaban kasa na Young Progressive Party (YPP), ya mayar da martani kan zargin da FBI ke yiwa Abba Kyari
  • Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana dalilin da ya sa batun Kyari ka iya shafar martabar Najeriya a duniya
  • Dan siyasar ya bayyana fatan cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi abin da ya dace kan lamarin

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Young Progressive Party (YPP), Kingsley Moghalu, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mutunta yarjejeniyar mika mutum tsakanin Najeriya da Amurka kan batun da ya shafi mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari.

Kotun Amurka ta nemi FBI ta gabatar da Kyari bisa zarginsa da hannu a zamba na miliyoyin daloli da Hushpuppi da sauran membobin kungiyarsa suka shirya.

Hushpuppi: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya gaya wa Buhari abin da ya kamata ya yi na mika Abba Kyari
Har yanzu Buhari bai ce komai ba kan lamarin Abba Kyari Hoto: Femi Adesina, Abba Kyari
Asali: Facebook

Da yake mayar da martani kan lamarin, Moghalu a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, 30 ga watan Yuli, ya ce dole ne a bari dokar kasa da kasa ta yi aikinta yadda ya dace, Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari a Landan: Burtaniya ta shirya taimakawa Najeriya a yaki da matsalar rashin tsaro

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriyan (CBN) ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta bi tsarin da ya dace a shari'ar da aka yi kan Kyari kamar yadda ta kama Nnamdi Kanu, shugaban 'yan asalin Biafra (IPOB), kuma ita ma tana neman a mika dan kabilar Yarbawa, Sunday Igboho, daga Jamhuriyar Benin.

Moghalu ya dage kan cewa yadda Buhari ya amsa bukatar FBI na mika Kyari a shari’ar Hushpuppi zai sanya Najeriya cikin fitinar duniya.

A cewarsa, Najeriya da Amurka sun kulla yarjejeniya ta fitar da mutane wanda aka yi amfani da ita a lokuta da dama.

Duk yunkurin bata sunan Abba Kyari da mutuncinsa ba zai yi aiki ba, Fani Kayode

A gefe guda, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya musanta zargin da ake yiwa DCP Abba Kyari bisa shiga cikin cakwakiyar amsar cin hanci daga hannun dan damfara Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kwararrun likitocin Najeriya za su tsunduma yajin aiki

Kamar yadda rahotonni suka gabata, Abba Kyari yana da hannu a cikin wata harka wacce dan damfara Hushpuppi ya kaddamar a Dubai inda ya samu fiye da dala 20,000 akan harkar, TheCable ta wallafa.

Otis Wright na Amurka ya umarci FBI ta kama Kyari ko ya bayyana a California yayi bayani akan shigarsa damfarar $1,124,426.36.

Asali: Legit.ng

Online view pixel