Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa asibiti a jihar Zamfara

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa asibiti a jihar Zamfara

  • Miyagun 'yan bindiga sun kutsa babban asibitin gwamnati na garin Dansadau dake karamar hukumar Maru a Zamfara
  • An gano cewa sun yi awon gaba da ma'aikaciyar jinya daya tare da wata mai jinyar mara lafiya a asibitin
  • Da farko sun fara kai farmaki garin Maigoge amma 'yan sa kai sun sakar musu ruwan wuta inda suka kashe wasu tare da raunata wasu

Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kutsa babban asibiti gwamnati dake Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Juma'a.

Daily Trust ta tattaro cewa miyagun sun yi awon gaba da wata ma'aikaciyar jinya da kuma wata mai jinyar mara lafiya.

KU KARANTA: DCP Abba Kyari: PDP ta ce bata son kumbuya-kumbuya, a bayyana komai

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa asibiti a jihar Zamfara
Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa asibiti a jihar Zamfara
Asali: Original

Ya ya harin ya faru?

Mazauna yankin sun sanar da cewa bayan 'yan bindigan sun shiga asibitin, 'yan bindigan sun fara neman likita ko ma'aikatan jinya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke 'yan bindiga 14, an damke masu kai musu bayanai 16, dabbobin sata 223

A yayin da basu samu kowa ba, sai suka fara shiga dakunan majinyata. Wata ma'aikaciyar jinya da mai jinyar mara lafiya suka sace. Daga nan suka nufi gidajen ma'aikata neman likitoci amma basu samu ba.
Tun farko 'yan ta'addan sun fara yunkurin kai farmaki Maigoge, yankin da ke da nisan kilomita shida daga arewacin garin Dansadau.
Amma a yayin da suka zagaye yankin, 'yan sa kai sun tsare kauyen. 'Yan sa kan sun kashe wasu daga cikin 'yan bindigan kuma sun raunata wasu.
Daga nan sun kutsa asibiti inda suka sace ma'aikaciyar jinya da likitocin da zasu duba raunikansu a daji.

Maigoge tana daya daga cikin yankunan dake masarautar Dansadau da aka san su da baiwa kansu kariya, Daily Trust ta wallafa.

Ma'aikatan asibitin basu aikin dare yanzu. Suna duba marasa lafiya ne da dare. Su kan shiga cikin garin su kwana a wuraren da ba a sani ba," ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Miyagu sun bi shahararren manomi har gonarsa sun sheke shi a Taraba

NMA reshen Zamfara ta magantu

A halin yanzu, shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar Zamfara, Dakta Mannir Bature, ya tabbatar da harin inda yace kungiyar tana cikin damuwa.

Ya ce asu yi taron gaggawa na ma'aikatansu a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel