Wasu Matasa 5 Da Ke Shirin Fara Yi Wa Ƙasa Hidima Sun Mutu a Hatsarin Mota a Abuja

Wasu Matasa 5 Da Ke Shirin Fara Yi Wa Ƙasa Hidima Sun Mutu a Hatsarin Mota a Abuja

  • Matasa biyar masu shirin fara yi wa kasa hidima sun rasu a hatsarin mota a Abuja
  • Matasan sun fito ne daga jihohin kudancin Nigeria suna hanyarsu na zuwa sansanin bada horaswa
  • Shugaba Muhammadu Buhari da hukumar NYSC sun mika sakon ta'aziyya ga iyalan matasan da suka rasu

FCT, Abuja - Wasu matasa biyar da ke shirin fara yi wa kasa hidima, NYSC, sun rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a ranar Laraba a babban hanyar Abaji zuwa Kwali a Abuja, The Cable ta ruwaito.

Masu shirin yi wa kasa hidimar suna kan hanyarsu ne na zuwa jihohin arewacin Nigeria domin hallartar horaswa na Batch B 2021 a yayin da hatsarin ya faru.

A cewar The Punch, kakakin NYSC, Adenike Adeyemi, ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne misalin karfe 2 na daren ranar Laraba 28 ga watan Yulin 2021.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

Wasu Matasa 5 Da Ke Shirin Fara Yi Wa Kasa Hidima Sun Mutu a Hatsarin Mota a Abuja
Shugaban hukumar NYSC Birgediya Janar Hassan Shu'aibu. Hoto: NYSC
Asali: Facebook

Hukumar ta NYSC, a sakon ta'aziyyar da ta fitar ta ce ta yi bakin cikin afkuwar hatsarin.

Buhari ya yi alhinin matasan masu zuwa sansanin NYSC da suka rasu

Kazalika, Femi Adesina, mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari ya ce shugaban kasar ya yi bakin ciki game da lamarin.

Sanarwar da ya fitar ta ce:

"Shugaban kasa yana taya hukumar NYSC da ma'aikatan ta yin ta'aziyyar wadanda suka rasu sakamakon hatsarin.
"Da ya ke mika ta'aziyya ga iyalan matasan, Shugaban kasar ya tabbatar musu cewa yan Nigeria sun taya su bakin ciki kuma za su cigaba da yi musu addu'a a wannan mawuyacin lokacin.
"Shugaban kasar ya mika fatan alheri ga dukkan masu yi wa kasa hidima da sabbin da aka kira zuwa sansanin bada horaswa a dukkan sassan kasar."

Buhari ya ce ba za a taba mantawa da sadaukarwar da jaruman suka yi ba.

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

Ya kara da cewa:

"Walwala da tsaron matasan Nigeria, da suka amsa kirar zuwa su yi wa kasarsu hidima za ta cigaba da kasancewa abin da zai rika bawa muhimmanci."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel