Gwamna Buni Ya Yi Watsi da Hukuncin Kotun Koli, Ya Na Nan Daram a Shugaban APC

Gwamna Buni Ya Yi Watsi da Hukuncin Kotun Koli, Ya Na Nan Daram a Shugaban APC

  • Gwamna Mai Mala Buni ka iya cigaba da zama a shugaban kwamitin riko na APC duk da rikicin da ya taso
  • Sakataren kwamitin riko na APC ta kasa, Sen. John Akpanudoedehe, shine ya faɗi haka a Abuja Ranar Alhamis
  • Akpanudoedehe yace za'a gudanar da tarurrukan jam'iyyar kamar yadda aka tsara duk da maganar wasu mambobin jam'iyyar

FCT Abuja - Sakataren kwamitin riko na jam'iyar APC ta ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya bayyana cewa gwamna Mai Mala Buni zai cigaba da jagorancin kwamitin riko na jam'iyyar.

Akpanudoedehe ya faɗi haka ne yayin taron manema labarai a sakateriyar APC ta ƙasa ranar Alhamis 29 ga watan Yuli.

Shugaban kwamitin riko, Mai Mala Buni tare da shugaba Buhari
Gwamna Buni Ya Yi Watsi da Hukuncin Kotun Koli, Ya Na Nan Daram a Shugaban APC Hoto: naijanews.com
Asali: UGC

Ya APC zata yi da hukuncin kotu?

Jaridar Punch ta ruwaito sakataren riko na APC yana cewa:

"Muna bayan shugaban mu na kasa, kuma zamu ɗora daga inda aka tsaya game tsare-tsaren tarurrukan mu kamar yadda aka shirya."

Kara karanta wannan

2023: ‘Yan Najeriya na Allah-Allah PDP ta dawo, In ji Atiku yayin da ya hadu da Wike don yin sulhu

A wani cikakken jawabi da aka aike wa Legit.ng sakataren yace:

"Hukuncin da kotun koli ta yanke ranar Laraba na tabbatar da nasarar gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu SAN, ba shi da alaka da matsayin kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC."
"Saboda haka muna kira ga mambobin jam'iyya da yan takara su fito kwanso da kwarkwata su bada gudummuwarsu a tarukan gunduma da zai gudana ranar Asabar mai zuwa."

Wani masanin doka ya yi tsokaci kan rikicin APC

A ɓangarensa, sanannen masanin doka, Kayode Ajulo, yace APC ka iya rasa duk wani kokarinta da ya biyo bayan ayyukan shugaban riko, Mai Mala Buni.

Vanguard ta rahoto Ajulo yana cewa da hukuncin da kotun koli ta yanke, duk wani zaɓe da APC ta gudanar wanda zai fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da na gwamnoni a babban zaɓen 2023 dake tafe ka iya zama mara amfani.

A wani labarin kuma Yan Najeriya Sama da Miliyan 60 Sun Mallaki Lambar NIN, NIMC

Kara karanta wannan

Masoya Atiku a jihar Kano sun fara rabawa Kanawa burodi da sunan kamfe

Hukumar NIMC ta ƙasa ta bayyana cewa zuwa yanzun yan Najeriya sama da miliyan 60m sun yi rijistar NIN.

NIMC ta bakin mai magana da yawunta, Mr. Kayode Adegoke, ta bayyana cewa a shirye take ta cigaba da samar da lambar ga yan ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel