Taimakonsa nayi, ban karbi ko sisi ba: Abba Kyari ya kare kansa kan zargin da Hushpuppi yayi masa

Taimakonsa nayi, ban karbi ko sisi ba: Abba Kyari ya kare kansa kan zargin da Hushpuppi yayi masa

  • Hazikin dan sanda yayi martani kan zargin karshen cin hancin da akayi masa
  • Gwamnatin Amurka ta ambaci sunan Abba Kyari cikin bincikenta
  • Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan labari

DCP Abba Kyari, ya karyata rahoton cewa ya karbi cin hanci hannun shahrarren dan damfara, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Huspuppi wanda ke kurkukun Amurka yanzu.

Jawabi daga gwamnatin Amurka ya nuna cewa Huspuppi ya lissafa Abba Kyari cikin jerin mutane shida da ya baiwa kudin cin hanci.

Amma a martani kan wannan tuhuma, Abba Kyari da safiyar Alhamis a shafinsa na IG ya ce bai taba tambayar Hushpuppi kudi ba kuma bai karbi kudi hannunsa ba.

Yace:

"Hushpuppi ya kira ofishinmu shekaru 2 da suka gabata cewa wani a Najeriya na barazanar kashe iyalinsa, inda ya turo mana lambar mutumin kuma ya rokemu mu dauki mataki kar a cutar da iyalansa."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Amurka Ta Bada Umurnin a Kamo Mata DCP Abba Kyari

"Sai muka bibiyi mutumin kuma muka damkesa, amma bayan bincike mun gano cewa babu wata barazana da ake yiwa kowa. Innama abokinsa ne suka sami rashin jituwa na kudi, sai muka sake sa bayan an karbi belinsa kuma bamu garkameshi ba."
"Babu wanda ya bukaci kudi hannun Abbas Hushpuppi kuma babu wanda ya karbi kudi hannunsa. Manufarmu itace kare rayukan mutane."

Abba Kyari ya kare kansa kan zargin da Hushpuppi yayi masa
Taimakonsa nayi, ban karbi ko sisi ba: Abba Kyari ya kare kansa kan zargin da Hushpuppi yayi masa Hoto: Abba Kyari
Asali: UGC

Abba Kyari ya kara da cewa daga baya Hushpuppi ya ga wasu kaya da huluna shafinsa, sai yace yana so kuma aka hadashi da mai sayar da kayan kuma ya turawa mai kayan kudi N300k."

"Sai aka kawo kayan ofishinmu kuma ya turo wani ya karba masa," ya kara.

DCP Abba Kyari na cikin wadanda na baiwa kudin cin hanci, Huspuppi

Mun kawo rahoton cewa Abbas Ramoni, wanda akafi sani da Huspuppi, ya bayyana cewa hazikin dan sanda, DCP Abba Kyari, na cikin wadanda ya baiwa kudin cin hanci.

Kara karanta wannan

Wani hamshakin attajirin Najeriya ya ziyarci kamfaninsa, ya baiwa ma'aikata manyan kudade a cikin bidiyo

Hakan na kunshe cikin wasu takardun kotun gwamnatin Amurka.

Bayan shekara da shekaru yana damfarar jama'a, an damke Hushpuppi a Dubai kuma aka garzaya dashi Amurka.

Jami'an kotu a Amurka sun ce yayin gudanar da bincike, Hushpuppi ya bayyana cewa ya baiwa Abba Kyari kudin cin hanci domin ya tayashi kulle wani dan adawarsa dake Najeriya kan harkallar damfarar wasu yan kasar Qatar $1.1 million.

A cewar jawabin da ma'aikatar Shari'ar Amurka ta saki, Huspuppi ya bukaci Abba Kayri ya kulle masa Kelly Chibuzor.

Asali: Legit.ng

Online view pixel