Da Dumi-Dumi: Yan Najeriya Sama da Miliyan 60 Sun Mallaki Lambar NIN, NIMC

Da Dumi-Dumi: Yan Najeriya Sama da Miliyan 60 Sun Mallaki Lambar NIN, NIMC

  • Hukumar NIMC ta ƙasa ta bayyana cewa zuwa yanzun yan Najeriya sama da miliyan 60m sun yi rijistar NIN
  • NIMC ta bakin mai magana da yawunta, Mr. Kayode Adegoke, ta bayyana cewa a shirye take ta cigaba da samar da lambar ga yan ƙasa
  • Hukumar ta yaba wa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Pantami, bisa kyakkyawan jagorancin da yake mata

FCT Abuja:- Hukumar samar da lambar ɗan kasa, NIMC, ranar Alhamis, ta sanar da cewa yan Najeriya sama da miliyan 60m sun yi rijistar lambar NIN, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Punch ta ruwaito cewa ya zuwa yanzun NIMC na da bayanan wannan adadin na yan Najeriya a ƙunshin ajiye bayananta (NIDB).

Hukumar ta kara da cewa an samu wannan nasarar ne da haɗin kan masu ruwa da tsaki a ɓangaren, wanda ya haɗa da gaba ɗaya yan Najeriya.

Yan Najeriya sama da miliyan 60m duna da lambar NIN
Da Dumi-Dumi: Yan Najeriya Sama da Miliyan 60 Sun Mallaki Lambar NIN, NIMC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kakakin hukumar NIMC ta kasa, Mr. Kayode Adegoke, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Kuna Yaudarar Kanku Ne, Jam'iyyar APC Ta Maida Martani Ga Gwamnonin PDP

Wani sashin jawabin yace:

"Hukumar NIMC na farin cikin sanar da cewa sama da yan Najeriya miliyan 60m sun yi rijistar lambar zama ɗan kasa NIN."
"A hukumance, mun gama duk wani shiri na rike wannan nasarar ta gudanar da rijistar katin zama ɗan ƙasa NIN a faɗin ƙasa baki daya."
"Hakan zai bada damar samun sahihan bayanan gane kowa, tantance kowa da kowa, da kuma ayyuka su rinka kaiwa ga kowane ɗan Najeriya."

Wane rawa Pantami ya taka?

Adegoke ya yaba wa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami, bisa kyakkyawan jagorancinsa wajen samun nasarar wannan aikin.

Ya ƙara jaddada cewa lambar NIN ita ce babbar hanyar da za'a samu bayanai da gane kowane ɗan Najeriya da kuma wanda doka ta ba shi damar zama a cikin ƙasa.

A wani labarin kuma Duk da Umarnin Kotu, DSS Ta Gaza Gurfanar da Hadiman Sunday Igboho Dake Tsare

Kara karanta wannan

Karo na Shida a Jere, FG Ta Sake Kara Wa'adin Hada Layin Waya da NIN, Ta Fadi Dalili

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi watsi da umarnin kotu na kawo hadiman shugaban yan awaren kafa kasar yarbawa, Sunday Igboho, gaban kotu.

Mai shari'a Obiora Egwuatu na babbar kotun tarayya dake Abuja ya umarci DSS ta gurfanar da hadiman Igboho 12 dake tsare a hannunsu ranar 29 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel