An tsaurara tsaro yayinda ake zaman yanke hukunci kan Sheikh Ibrahim ElZakzaky da Matarsa yau

An tsaurara tsaro yayinda ake zaman yanke hukunci kan Sheikh Ibrahim ElZakzaky da Matarsa yau

  • Ana kyautata zaton yau za'a yanke hukuncin karshe kan Zakzaky da Matarsa
  • An tsare babban Malamin tun watan Disamban 2015
  • Hakan ya biyo bayan rikicin da ya auku tsakanin mabiyan Malamin da Sojoji

Kaduna - A yau Ranar Laraba ake sa ran babban kotun jihar Kaduna karkashin Alkali Gideon Kurada za ta yanke hukunci kan shugaban IMN, Sheikh Ibrahim Zakzaky da Matarsa, Zeenat Ibrahim.

Shekara hudu kenan suna gurfana da kotu.

Wannan na kunshe cikin jawabin da shugaban yada labaran kungiyar IMN, Ibrahim Musa, ya saki ranar Talata a Kaduna, rahoton Leadership.

Musa ya ce ana kyautata zaton kotun ta amsa bukatar lauyan Zakzaky, Femi Falana, na watsi da karar saboda cikin dukka shaidu 15 da lauyoyin gwamnati suka kira, babu wanda ya bada gamsasshen hujja kan laifukan da ake zargin Zakzaky da su.

Gwamnatin jihar Kaduna ta tuhumi El-Zakzaky da Zeenat da laifuka takwas, wanda suka hada da kisan kai, tayar da tarzoma, dss.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Yadda Kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa, ta umarci a sake su

Zakzaky da Matarsa sun ce karya akayi musu.

Yau za'a yanke hukunci kan Sheikh Ibrahim ElZakzaky da Matarsa
Yau za'a yanke hukunci kan Sheikh Ibrahim ElZakzaky da Matarsa Hoto: Zakzaky da Zeenat
Asali: Facebook

Zaman karshe da kotun tayi

A zaman karshe da kotun tayi ranar 1 ga Yuli, Kamfanin dillancin labarai NAN ta rahoto Lauyan Zakzaky, Femi Falana, wanda yayi hira da manema labarai bayan zaman kotun ya bukaci kotun ta baiwa Zakzaky nasara.

Za ku tuna cewa a wasu kotuna biyu da aka gurfanar da Zakzaky a baya, duk an yi watsi da tuhumar da ake musu.

Daga ciki har da wanda aka bada umurnin sakin mambobin kungiyar kimanin 200.

Asali: Legit.ng

Online view pixel