‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe Sojojin kasar Kamaru a wasu sababbin hare-hare

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe Sojojin kasar Kamaru a wasu sababbin hare-hare

  • ‘Yan Boko Haram sun kashe wasu jami’an sojoji a yankin Arewacin kasar Kamaru
  • An samu sojoji uku da farar hula daya da ‘Yan ta’addan su ka ji wa rauni a kasar
  • Kafin yanzu, sojojin ISWAP da Boko Haram sun kashe jami’an tsaro a garin Sagbe

Kamaru - ‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin kasar Kamaru biyar da wani mutum guda a wani hari da suka kai a Arewacin kasar.

Jaridar Punch ta bayyana cewa ma’aikatar tsaron kasar Kamaru ta tabbatar da wannan hari a jiya.

An kuma hallaka wasu sojojin kasar Kamaru

‘Yan ta’addan sun yi wannan ta’adi ne a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli, 2021, a daf da iyakar Najeriya da kasar ta Kamaru da ta ke makwabtaka da ita.

Sojoji har uku da wani farar hula guda suka samu rauni daga wannan mummunan hari kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar wajen ta fitar a wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Duka Ma’aikatan fadar Shugaban kasa sun dauki rantsuwar hana sirri fita daga Aso Rock

“Gungun wasu ‘yan ta’addan Boko Haram dauke da manyan makamai sun hau motoci, sun kai wa jami’an tsaro hari a kusa da Zigue, kilomita kadan zuwa Najeriya.”
“Dakaru sun farga a yankin Arewa da kan iyaka domin hana a kawo wasu sababbin hare-haren.”

Sojojin kasar Kamaru
Dakarun Sojojin kasar Kamaru Hoto: www.thedefensepost.com
Asali: UGC

Ma’aikatar tsaron kasar take cewa bisa dukkan alamu, sojojin Boko Haram suna kara karfi bayan wasu gyare-gyaren cikin gida da kungiyar ta’addan ta yi.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan ta’addan sun kashe sojoji takwas a garin Sagme a ranar Asabar. Shi ma wannan gari ya na kan iyaka ne da kasar Najeriya.

‘Yan Boko Haram sun addabi kasashen Afrika ta yamma

VOA ta ke cewa Mayakan Boko Haram da Islamic State in West Africa sun matsa wa yankin Arewacin Kamaru lamba musamman a ‘yan kwanakin nan.

Kananan yara da mata ne su ka fi fada wa hannun ‘yan ta’addan a yankin Kamaru, Nijar, Chadi da Najeriya. ‘Yan ta’addan su kan tsere da mata da kuma yaran.

Kara karanta wannan

Ramuwar gayya: ‘Yan bindiga sun auka wa wani kauye a Zamfara, sun hallaka dinbin mutane

A wani tsohon faifai da aka samu, an ji shehin malamin musuluncin nan, Dr. Ahmad Gumi ya na cewa barnar da aka yi a mulkin Jonathan ba ta kai ta yanzu ba.

Ahmad Gumi ya ce ko dai ya ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri, ko kuma ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga kan mulkin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel