Dattijon da Yaje Kai Kudin Fansa Miliyan N30m Ya Kubuta, Ya Fadi Halin da Daliban Islamiyyar Tegina Ke Ciki

Dattijon da Yaje Kai Kudin Fansa Miliyan N30m Ya Kubuta, Ya Fadi Halin da Daliban Islamiyyar Tegina Ke Ciki

  • Mutumin da yan bindiga suka riƙe daga kai kuɗin fansa miliyan N30m ya dawo
  • Kasimu Barangana ya bayyana cewa ɓarayin sun ba shi kulawa yadda ya kamata lokacin zamansa a wurinsu
  • Yace ɗaliban an kasa su wurare 25 kuma yanayin da suke ciki babban abin damuwa ne

Tegina, Niger:- Mutumin da yaje kai kuɗin fansa ga ɓarayin da suka sace ɗaliban islamiyyar Tegina, jihar Neja ya kuɓuta daga hannunsu.

Sahara Reporters ta ruwaito yadda yan bindigan suka riƙe Kasimu, daga zuwa kai kuɗin fansa saboda a cewarsu kuɗin basu cika miliyan N30m ba.

Dattijon ya bayyana cewa ɗaliban suna cikin mummunan hali a hannun yan bindigan da suka sace su.

A ranar 30 ga Mayu yan bindiga suka yi awon gaba da ɗalibai da yawa daga makarantar Salihu Tanko Yakasai dake Tegina, karamar hukumar Maru.

Dattijon da Yaje Kai Kudin Fansa Miliyan N30m Ya Kubuta, Ya Fadi Halin da Daliban Islamiyyar Tegina Ke Ciki
Dattijon da Yaje Kai Kudin Fansa Miliyan N30m Ya Kubuta, Ya Fadi Halin da Daliban Islamiyyar Tegina Ke Ciki Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A wane wuri suka ɓoye ɗaliban?

Kasimu Barangana ya shaidawa premium times bayan an sako shi ranar Litinin cewa ɓarayin sun aje ɗalibai a wurare 25 cikin yanayi mara dadi.

Kara karanta wannan

Dakarun Soji Sun Damke Mutum 19 Dake Tallafawa Yan Bindiga a Jihar Zamfara

Yace: "An kaini dukkan wuraren domin ganin yaran kuma na gansu cikin yanayi abun damuwa da tashin hankali."

Ɓarayin sun cutar dakai yayin da kake hannunsu?

Barangana ya bayyana cewa yan bindigan sun kyautata masa yayin da yaje dajin, sun kula da shi yadda ya kamata.

Yace: "Lokacin da nake cikin dajin tare da masu garkuwa da mutane, sun kula da ni yadda ya kamata, ana bani abinci isasshe. Da zan dawo suka bani dubu 11,000 in yi kuɗin mota."

Yaushe zasu sako daliban?

Mutumin yace ba zai iya faɗin ranar da masu garkuwa zasu sako yaran ba, kawai a cigaba da addu'a Allah ya dawo da su lafiya.

Yace: "Mu cigaba da addu'ar dawowar yaran mu cikin ƙoshin lafiya amma ba zai iya faɗin ranar da zasu sako su ba saboda yanzun suna neman mashin guda biyar a matsayin wata fansa."

A wani labarin kuma Gwamnatin Benin Ta Sake Maka Sunday Igboho a Kotu da Sabbin Tuhuma

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: El-Rufa'i Ya Dakatad da Komawa Makaranta a Jihar Kaduna Sai Baba Ta Gani

Yayin da ake cigaba da shari'ar Igboho, gwamnatin jamhuriyar Benin ta sake shigar da sabbin tuhume-tuhume a kan ɗan awaren yarbawa, Sunday Igboho.

Punch ta ruwaito cewa ɗaya daga cikin lauyoyin dake kare Igboho, Ibrahim Salami, yace tawagar su na tsammanin fara shari'ar ɗan fafutukar da gwamnatin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel