Wata sabuwa: Kwararrun likitocin Najeriya za su tsunduma yajin aiki

Wata sabuwa: Kwararrun likitocin Najeriya za su tsunduma yajin aiki

  • Kungiyar kwararrun likitoci a Najeriya ta ce za ta tsunduma yajin aiki nan kusa cikin kwanaki 21
  • Kungiyar ta koka kan yadda aka cire wasu likitoci kan tsarin biya na bai daya na ma'aikatar wato CONMESS
  • Kungiyar ta ce cirewar ta jawo baraka da cikas da koma baya bangaren aikin likitanci a Najeriya

Kungiyar Kwarrarun Likitoci ta MDCAN a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aiki na sai baba ya gani kan wata bukata da ta ke dashi na gyara tsarin albashin mambobinta, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban MDCAN na kasa, Farfesa Keneth Ozoilo, ya ba da wa’adin kwanaki 21 na shiga yajin aiki a taron manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato, ranar Litinin, 26 ga watan Yuli.

Ya ce an yanke shawarar bayar da wa'adin ne yayin taron gaggawa na kungiyar ta kasa da aka gudanar a ranar 19 ga Yulin 2021.

Wata sabuwa: Kwararrun likitocin Najeriya za su tsunduma yajin aiki
Likitoci na aiki | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ozoilo ya koka kan cewa umarnin cire likitocin da ke koyarwa a jami'o'i daga tsarin albashi na bai daya (CONMESS) ya haifar da koma baya a aikin.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: Kungiyar ASUU za ta iya komawa dogon yajin-aikin da ta dakatar a 2020

Ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta janye wannan umarnin ko kuma su shiga yajin aiki sai baba ya gani.

A baya nan: 'Yan majalisa sun fusata, sun baiwa Shugaban MDCN awa 24 ya bayyana gabansu

Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kiwon lafiya ya yi barazanar bada izinin kamo shugaban hukumar dake kula da likitocin ƙasar nan (MDCN), Tajudeen Sanusi, matuƙar bai bayyana a gabansu ba gobe Jumu'a.

An gayyaci Sanusi da ya bayyana a gaban kwamitin domin ya amsa wasu tambayoyi akan yajin aikin da ƙungiyar likitoci (NARD) ke yi.

Sai dai bisa dole yan majalisar wakilan dake cikin kwamitin suka ɗage taron bayan sun samu masaniyar cewa Sanusi na can ya halarci kotun hukumarsa, in ji wani rahoton Daily Trust.

Shugaban kwamitin, Hon. Tanko Sununu ya ce Sanusi bai girmama gayyatar mu ba wacce take ta gaggawa amma yaje can ya halarci abinda ransa ke so.

Kara karanta wannan

Rimingado zai yi karar likitan da ya bashi shaidar asibiti ta bogi

Ɗan majalisa Sununu ya ce:

"Mun aika da gayyatar mu ga dukkan masu ruwa da tsaki da su halarci wannan taron, amma sai aka yi rashin sa'a shi yaƙi zuwa.
"Saboda shine ginshiƙin taron, dole tasa muka ɗage taron daga yau, muka kira shi da ya bayyana a gabanmu kafin karfe 9:00 na safiyar gobe Jumu'a.
"Idan kuma yaki zuwa a wannan lokacin da muka bashi to zamu yi amfani da ƙarfin majalisar ƙasar nan mu ɗauki matakin doka akansa, wanda ya haɗa da bada izinin kamo shi duk inda yake."

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudi N982Bn, karin kan na 2021

A wani labarin, Shugaban kasar Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari (Mai ritaya) ya rattaba hannu kan kasafin kudin da ya kai N982.7bn, kari kan na shekarar bana ta 2021 domin warware wasu matsaloli da kasar ke fuskanta.

Wannan ya fito ne daga wata sanarwa mai magana yawun shugaban kasa , Garba Shehu ya fitar a yau Litinin 26 ga watan Yuli, 2021, wacce Legit,ng Hausa ta samo.

Kara karanta wannan

Bayan Kame Sunday Igboho, Yarbawa sun magantu kan ra'ayin ballewa daga Najeriya

Sanarwar ta bayyana cewa, karin kasafin kudin za a yi amfani dasu ne wajen warware matsalolin tsaro da kuma annobar Korona da kasar ke fuskanta.

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin a Abuja ya rattaba hannu kan karin kasafin kudi na N982.7bn na 2021 don magance matsalar tsaro cikin gaggawa da bukatun Korona na kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel