Sarkin Fulani Ya Yi Magana Kan Shari'ar Igboho a Benin, Ya Bukaci Gwamnati Ta Taso Keyar Shi Zuwa Najeriya

Sarkin Fulani Ya Yi Magana Kan Shari'ar Igboho a Benin, Ya Bukaci Gwamnati Ta Taso Keyar Shi Zuwa Najeriya

  • Sarkin Fulanin Igangan ya buƙaci gwamnatin tarayya data dawo da shari'ar Sunday Igboho Najeriya
  • Alhaji Abdulkadir, yace dukkan laifukan da ake tuhumarsa a kai ya aikata su ne a ƙasar nan
  • Sarkin Fulani Abdulkadir yace ba tare da bincike ba an umarce shi ya bar Igangan, inda ya kwashe shekara 50

Sarkin Fulanin Igangan, jihar Oyo, Alhaji Salihu Abdulkadir, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dawo da shugaban yan awaren yarbawa, Sunday Adeyemo Igboho daga jamhuriyar Benin zuwa Najeriya.

Abdulkadir, wanda ya zanta da leadership a Ilorin, jihar Kwara, ya bayyana cewa dawo da Igboho Najeriya ya zama wajibi saboda laifin da ake tuhumarsa da shi a Najeriya ya aikata su.

Ya zargi shugabannin yarbawa da gaza tsawatar masa yayin da tawagarsa ke aikata ta'adddanci akan mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba, kawai don su fulani ne.

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

Sunday Adeyemo Igboho
Sarkin Fulani Ya Yi Magana Kan Shari'ar Igboho a Benin, Ya Bukaci Gwamnati Ta Taso Keyar Shi Zuwa Najeriya Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Sai dai duk da buƙatar da FG ta tura na dawo da Igboho Najeriya, kotun kwatano taƙi amincewa da hakan, kamar yadda sahara reporters ta ruwaito.

Tawagar Igboho na kai wa Fulani hari

Abdulkadir ya ƙara da cewa wasu mutane sun bukaci ɗan fafutukar awaren da ya kai wa fulani hari.

Yace: "Duk masu goyon bayan Igboho a kan kashe mutanen da ba su ji ba kuma basu gani ba zasu ɗauki darasi idan suka girbi abinda suka shuka."

"Igboho ya yi ikirarin cewa mutanen Igangan sun nemi da ya kaiwa yankunan da fulani ke zaune hari."

"Muna sane cewa shugabannin yarbawa suna sane da manufar Igboho saboda ya kamata su taka masa birki amma ba su yi hakan ba."

Shekara 50 Ina rayuwa a Igangan

Sarkin Fulani Abdulkadir ya musanta duk wasu zarge-zarge da aka ɗora akan shi, inda yace:

"Ba tare da gudanar da sahihin bincike ba an bani wa'adin mako ɗaya in bar Igangan, wurin da na shekara 50 ina rayuwa."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

"A najeriya ya kamata a yi shari'ar Igboho, tunda dukkan laifukan da ya aikata yayi su ne a jihohin Oyo, Ondo da kuma Ogun."

A wani labarin kuma Yan Najeriya Miliyan 85m Zasu Rasa Aikinsu, Inji Ministan Buhari Ya Fadi Dalili

Ƙaramin ministan kimiyya da fasaha, Mr. Mohammed Abdullahi, ya bayyana cewa kimanin yan Najeriya miliyan 85m suna kan siraɗin rasa ayyukansu saboda rashin ilimin fasahar zamani da kwarewa.

Ministan ya faɗi haka ne a wurin taron kaddamar da shirin samarwa matasa yan Najeriya miliyan 20m ayyukan yi daganan zuwa shekarar 2030.

Asali: Legit.ng

Online view pixel