Kuna Yaudarar Kanku Ne, Jam'iyyar APC Ta Maida Martani Ga Gwamnonin PDP

Kuna Yaudarar Kanku Ne, Jam'iyyar APC Ta Maida Martani Ga Gwamnonin PDP

  • Jam'iyyar APC ta ƙasa ta maida martani ga jawabin da gwamnonin PDP suka fitar bayan taron su a jihar Bauchi
  • APC ta bayyyana cewa ya kamata jam'iyyar adawa PDP ta daina yaudarar kanta game da dalilin da yasa ƴaƴanta suke gudunta
  • A cewar APC, kyakkyawan mulkin shugaba Buhari ne yake janyo hankalin yan adawa suna shigowa jam'iyya mai mulki

Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa gamsuwa da mulkin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ne yake jawo hankalin gwamnonin PDP su sauya sheƙa zuwa APC, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Jam'iyya mai mulki tace wannan "Yaudarar kai ne" PDP ta cigaba da tsammanin cewa yayan ta zasu cigaba da zama a cikinta duk da gazawar da ta yi.

Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga jawabin da gwamnonin PDP suka fitar bayan taron su da ya gudana a Bauchi ranar Litinin, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP: Buhari ya mayar da fadar shugaban kasa sakateriyar APC

APC da PDP
Kuna Yaudarar Kanku Ne, Jam'iyyar APC Ta Maida Martani Ga Gwamnonin PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A jawabin, Gwamnonin sun zargi APC da amfani da ƙarfin mulki wajen tilastawa mambobinta sauya sheƙa.

A martanin da yayi, sakataren kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC ta ƙasa, John Akpanudoedehe, yace:

"An jawo hankalin mu kan wasu maganganu da gwamnonin PDP suka yi wanda ya ƙunshi karya da ragwancin su a halin da kasa ke ciki."

"Muna kara jaddada cewa PDP na yaudarar kanta ne idan tana tsammanin ƴaƴanta zasu cigaba da nutsewa a cikinta duk da gazawar da jam'iyyar ta yi."

"Ya kamata PDP tasan cewa mambobinta da shugabanninta suna sauya sheka zuwa APC ne saboda gamsuwa da mulkin jam'iyar APC na shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da kuma kyakkyawan jagorancin gwamna Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya na APC."

Buhari ya kawo cigaba a ɓangaren zaɓe

Sakataren APC ya ƙara da cewa duk wani zaɓe da aka gudanar ƙarƙashin mulkin shugaba Buhari zakaga akwai cigaba da aka samar a cikinsa.

Kara karanta wannan

Ku Mun Adalci Wajen Rubuta Nasarori Na, Shugaba Buhari Ga Marubuta Tarihi

Yace: "A zamanin mulkin shugaba Buhari, duk wani zaɓe da aka gudanar an samu cigaba sosai a ciki. APC zata cigaba da goyon bayan hukumar zaɓe a dokance domin gudanar da sahihin zaɓe a idanun duniya."

"A cikin jam'iyya, APC ta gudurta yin adalci ga kowa a duk wani mataki da zata ɗauka musamman wajen zaɓen shugabanninta da zaɓen fidda gwani."

A wani labarin kuma Ina Rayuwa a Karamin Gida Cikin Talakawa, Gwamna Ya Fadi Inda Yake Rayuwa Duk da Matsayinsa

Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia , yace yana rayuwa ne a gida mai ɗakin kwana uku a Aba, babbar cibiyar kasuwancin jihar.

Ya ƙara da cewa ya zaɓi rayuwa a cikin mutanen da yake mulka ne domin yasan akwai wata rayuwar bayan ya kammala mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel