Ubangiji ya juyawa Buhari baya, Fasto Bakare ya bayyana a sabon bidiyo

Ubangiji ya juyawa Buhari baya, Fasto Bakare ya bayyana a sabon bidiyo

  • Fasto Tunde Bakare ya fitar da sabon bidiyo inda yace Ubangiji ya juyawa Buhari baya
  • Kamar yadda yace, zai yaki shugaban kasan, idan an so a bibiyeshi kamar yadda aka saba yi
  • Faston ya bayyana yadda yaso Buhari, mutunta shi, bauta mishi amma ya watsa mishi kasa a ido

Oregun, Lagos

Tunde Bakare, shugaban cocin Citadel Global Community, ya ce Ubangiji ya juyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.

A yayin jawabi a cocinsa wacce a da aka sani da Latter Rain Assembly, Bakare yace zai yi fito-na-fito da shugaban kasa kuma ya ga wanda zai bibiyesa kamar yadda aka saba yi wa duk wanda yayi magana a kasar nan.

KU KARANTA: Ina bukatar miji, Budurwa mai son daidaituwar 'yancin mata da maza ta koka

Ubangiji ya juyawa Buhari baya, Fasto Bakare ya bayyana a sabon bidiyo
Ubangiji ya juyawa Buhari baya, Fasto Bakare ya bayyana a sabon bidiyo. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Ruwan daloli: Bidiyon bahaushe yana watsi da daloli a liyafar biki ya janyo cece-kuce

Dole ne mu tashi tsaye mu kwaci hakkinmu

Kara karanta wannan

Zan iya ziyartar Daura duk makonni biyu kuma babu wanda zai iya hana ni, Buhari

Karfin iko ba a hannunka yake ba, kaine dai mai baiwa dakarun sojin kasa umarni, kuma baka isa ba idan ba a zabeka ba. Babban ofishi a kasar nan shine na dan kasa. 'Yan Najeriya zasu tashi kuma su bukaci hakkinsu
"Kuma idan ka isa ka yi kokarin kawo hannunka kaina kamar yadda kake yi wa sauran, a nan ne zaka gane ko Ubangiji ne ya turo ni ko kuma surutu kawai nake yi.
Lokacin ceto kasar nan yayi. Gwamnati ba zata iya ceton mu ba, dakarun soji ba zasu iya ba, dole ne mu tashi mu nemi hakkinmu.

Na yi maka halacci amma ka watsa min kasa a ido

Ku fita daga hanyata, ku fita daga idona, wannan ne jan kunne na karshe. Na so ka, na yi maka bauta, na mutunta ka, na yi komai don ganin nasarar ka amma ka juya min baya kuma Ubangiji ya juya maka. Ka fita daga hanyata.

Kara karanta wannan

Rashin tashin bam ko 1 yayin sallah alamace ta dawowar ingancin tsaro, Fadar Buhari

Bakare ya ce ya sanar da Buhari kafin 2014 cewa zai zama shugaban kasa kuma ya sanar da shi takamaiman abinda zai faru, amma yanzu ya juya masa baya, Bakare ya fadi a wani bidiyo.

A wani labari na daban, masu garkuwa da mutane dake barna a babban birnin tarayya (FCT) suna cigaba da habaka saboda sun fara karbar kudin fansa ta hanyar amfani da asusun bankunansu, Daily Trust ta ruwaito.

A makon da ya gabata, Daily Trust ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da mutane har kashi biyu a yankin Tungan Maje dake wajen garin. Miyagun sun koma yankin a ranar Laraba bayan sun sace mutum 6 daga yankin.

Sauran yankunan babban birnin tarayya da suka hada da Kuje, Bwari da Abaji suna fuskantar hauhawar lamarin garkuwa da mutane a watanni kadan da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel