Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

  • Alkalin kotun daukaka kara a Kwatano ya bada umurnin a tafi da Sunday Igboho gidan yari
  • Hakan na zuwa ne bayan kotun ta shafe kimanin awanni 13 tana sauraran shari'ar Sunday Igboho
  • Ana tuhumar dan gwagwarmayar ne da laifuka masu alaka da safarar makamai, tada rikici da sauransu

Kotun Jamhuriyar Benin da ke zamanta a Kwatano ta tura Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho zuwa gidan yari, The Cable ta ruwaito.

An kammala zaman kotun ne misalin ƙarfe 11.20 na daren ranar Litinin bayan shafe kimanin awanni 13.

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano
Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano
Asali: Original

Wani majiya daga kotun ta shaidawa The Cable cewa ba za a saki Igboho ba.

"Matsalar mayar da wanda ake zargin da laifi ƙasarsa domin ya fuskanci sharia lamari ne da akwai siyasa sosai a cikinsa."

Majiyar ta kara da cewa Igboho ya yi ta rokon kotun kada ta mayar da shi Nigeria saboda yana tsoron akwai yiwuwar a kashe shi.

Kara karanta wannan

Jerin sabbin manyan laifuka 3 da jamhuriyar Benin ke tuhumar Sunday Igboho akai

Har yanzu ba a gama samun cikakken rahoto game da hukuncin ba, amma majiyar ta kara da cewa hukuncin kotun na nufin da nan take za a dawo da Igboho Nigeria ba inda ake nemansa ruwa a jallo.

Amma, ba a sani ba idan gwamnatocin kasashen biyu za su iya cimma yarjejeniyar siyasa a yayin da Igboho ke tsare.

An hana yan jarida, masu sarautar gargajiya da magoya bayan Igboho da suka zo ganin yadda Shari'ar zata kaya shiga kotun.

Sun tsaya a harabar kotun har zuwa misalin ƙarfe 7 na yamma a yayin da jami'an tsaro dauke da makamai suka iso suka kori duk wanda kotu bata gayyace shi ba.

An kama Igboho da matarsa, Ropo, ne a filin tashin jirage a Kwatano a makon da ta gabata sannan aka tsare su a kan umurnin gwamnatin Nigeria.

Lauyoyinsa sun bukaci a saki matarsa a kan cewa bata yi wa gwamnatin Nigeria laifi ba.

Kara karanta wannan

Hatta Musa Ya Yi Hijira Saboda Fir'auna, Babu Laifi Don Igboho Ya Tsere, Afenifere

A ranar Alhamis, kotu ta amsa bukatarsu ta bada umurnin a sake ta a kuma mayar mata fasfo ɗin ta.

An tafi an tsare Igboho inda aka ajiye shi har zuwa ranar Litinin.

An tuhumi ɗan gwagwarmayar Yarbawan da laifuka da suka shafi safarar makamai, tada rikici da neman ɓallewa daga Nigeria don kafa ƙasar Yarabawa.

Igboho da lauyoyinsa sun musunta wannan zargin.

Malamin Sunday Igboho Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Yi ‘Layar Zana’ Ba, Ya Bari Aka Kama Shi

A wani labarin daban, Idris Oladejo, malamin Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana dalilin da yasa mai rajin kafa Kasar Yarbawan bai yi kayan zana ya bace daga hannun jami'an tsaro ba.

Da ya ke magana da The Cable a kotun daukaka kara a Jamhuriyar Benin a Kwatano, malamin da aka fi sani da Imam Oladejo, ya ce Igboho bai bace daga hannun jami'an tsaro bane saboda matarsa da Kasar Yarbawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sunday Igboho ya isa kotu a Kwatano don sanin makomarsa

A lokacin da jami'an tsaro suka kai samame gidan Igboho a farkon watan Yuli, an ce dan gwagwarmayar ya ce amfani da asiri ne ya bace ba su kama shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel