Yanzu-Yanzu: Sunday Igboho ya isa kotu a Kwatano don sanin makomarsa

Yanzu-Yanzu: Sunday Igboho ya isa kotu a Kwatano don sanin makomarsa

  • A ranar Litinin aka gurfanar Sunday Igboho a gaban kotun jamhuriyar Benin don jin yiyuwar mika shi ga Najeriya
  • An kawo Sunday Igboho kotu tun karfe 7 na safe, haka kuma ba a saurare shi ba har kusan karfe 12
  • Najeriya na bukatar a dawo da Sunday Igboho Najeriya domin fuskantar shari'a kan wasu laifukan cin amanar kasa

A yau ne Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa ya bayyana a Kotun daukaka kara a Kwatano inda yake gab da fuskantar shari'a, The Nation ta ruwaito.

Ko da yake an kawo shi kotu kuma an ajiye shi a daki tun 7 na safe, amma har yanzu ba a fara shari’arsa ba da misalin karfe 11.55 na safe.

Yanzu-Yanzu: Sunday Igboho ya isa kotu a Kwatano don sanin makomarsa
Dan Awaren Yarbawa, Sunday Igboho | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Magoya bayan sa sun yiwa kotun kawanya suna jiran a fara shari’ar.

Matarsa, Ropo, da daruruwan magoya bayansa, ciki har da wasu sarakunan gargajiya na Yarbawa, suna cike da damuwa kan yadda abin zai kasance na bukatar mika shi ga gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu zuwa wani lokaci, zai ci gaba da zama a DSS

A Najeriya kuwa, Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta dage shari’ar Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar tsageru IPOB saboda gazawar Gwamnatin Najeriya na gurfanar da shi a gaban kotu ranar Litinin, in ji Channels Tv.

Lokacin da aka dago batun, lauya mai gabatar da kara, M. B. Abubakar, ya sanar da kotu cewa an shirya sauraren karar kuma a shirye suke su ci gaba.

Amma lauyan Nnamdi Kanu, Ifeanyi Ejiofor, ya sanar da kotu cewa akwai karar da ake jira a gaban kotu don a sauya Kanu daga tsarewar hukumar DSS zuwa cibiyar gyaran hali.

Mai shari’a Binta Nyako ta bayyana cewa ba za a ci gaba da shari’ar ba ba tare da shugaban IPOB din a wirin ba tunda ba shi da damar tsayawa kan shari’ar tasa.

Kara karanta wannan

Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu zuwa wani lokaci, zai ci gaba da zama a DSS

An saki Sowore da magoya bayan Nnamdi Kanu bayan sun ci duka

A wani labarin, Rahoto ya bayyana cewa, an saki mawallafin jaridar SaharaReporters Omoyele Sowore da wasu da aka kama yayin wata zanga-zanga a Babbar Kotun Tarayya, jaridar Punch ta ruwaito.

Masu fafutukar sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda ke fuskantar shari'a a kotu.

‘Yan sa’o’i kadan bayan kamasu, dan fafutukar 'Buhari-Must-Go' ya sanar da cewa an sake shi tare da wasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel