Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan IPOB a Wurin Shari'ar Nnamdi Kanu

Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan IPOB a Wurin Shari'ar Nnamdi Kanu

  • Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, wasu mambobin kungiyar IPOB sun mamaye bakin babban kotun tarayya a Abuja
  • Sai dai, tuni 'yan sanda suka fatattake su, yayin da aka yi ram da wasu da dama daga cikinsu
  • A yau ne za a zauna domin daddale hukuncin Nnamdi Kanu, wanda ake zargi da cin amanar kasa

‘Yan sanda a ranar Litinin sun fatattaki wasu mambobin kungiyar IPOB wadanda suka mamaye Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja don jin yadda za ta kaya a shari’ar Nnamdi Kanu, shugabansu.

Mambobin kungiyar da suka fusata sun mamaye kotun gabanin shari’ar tasa, inda wani rahoton The Cable ya ce tuni an kame wasu daga cikin mambobin na IPOB.

‘Yan kungiyar IPOB din suna ta rera taken nuna goyon baya ga Kanu tare da neman a sake shi.

Da Duminsa: 'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan IPOB a Wurin Shari'ar Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu a daure | Hoto: saharareporters.com

Biyu daga cikinsu sun sanya tufafin yahudawa.

Wani mutum sanye da bakaken kaya harma yayi wa wasu manema labarai jawabi amma yayi magana ne da yaren Igbo, inji Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai

Sai dai, yayin da yawansu ya karu, ‘yan sanda suka afka wurin suka fatattake su.

Ba a kawo Kanu kotu ba har zuwa lokacin da aka shigar da wannan rahoton.

Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai

Akwai yiwuwar Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB, dake fuskantar manyan laifuka da hukuncinsu ya kai ga hukuncin kisa ko daurin rai da rai yayin da za a ci gaba da shari’arsa a yau Litinin, 26 ga watan Yuli.

Gwamnatin tarayya a cikin wata wasika da ta aika wa jami’an diflomasiyyar kasashen yamma ta zargi shugaban na IPOB da aiwatar da kashe-kashen jama’a a kasar.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, gwamnatin ta ce Kanu ya shirya kisan mutane akalla 60 da lalata dukiyoyi a wasu hare-hare 55 da aka kai hari a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu cikin watanni hudu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

Wasikar wacce ke dauke da kwanan watan 26 ga Afrilu, 2021, ta yi zargin cewa mambobin kungiyar IPOB ne suka aikata ta'asar a kan umarnin da aka ce Nnamdi Kanu ne ya bayar a lokacin da yake boye a Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel