Masu garkuwa da mutane a Abuja sun fara karbar kudin fansa ta banki

Masu garkuwa da mutane a Abuja sun fara karbar kudin fansa ta banki

  • Masu garkuwa da mutane suna cigaba da cin karensu babu babbaka a babban birnin tarayyar Abuja
  • A halin yanzu sun daina karbar kudi kai tsaye, sun koma bukatar a saka musu ta asusun banki
  • Amina Adewuyi an saceta a Madalla kuma masu garkuwa da mutanen sun bada lambar asusun banki a saka musu kudin fansa

FCT, Abuja

Masu garkuwa da mutane dake barna a babban birnin tarayya (FCT) suna cigaba da habaka saboda sun fara karbar kudin fansa ta hanyar amfani da asusun bankunansu, Daily Trust ta ruwaito.

A makon da ya gabata, Daily Trust ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da mutane har kashi biyu a yankin Tungan Maje dake wajen garin. Miyagun sun koma yankin a ranar Laraba bayan sun sace mutum 6 daga yankin.

Sauran yankunan babban birnin tarayya da suka hada da Kuje, Bwari da Abaji suna fuskantar hauhawar lamarin garkuwa da mutane a watanni kadan da suka gabata.

Kara karanta wannan

Allah Ya Isa Ban Yafe Ba, Fitacciyar Jarumar Kannywood Ta Yi Martani Ga Masu Sukarta

KU KARANTA: Igboho ya maka FG a kotu, yana bukatar N5.5bn na diyyar kutse a gidansa

Masu garkuwa da mutane a Abuja sun fara karbar kudin fansa ta banki
Masu garkuwa da mutane a Abuja sun fara karbar kudin fansa ta banki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnan Gombe na makokin manjon soja, matarsa da diyarsa da hatsari ya kashe

An fara karbar kudi ta yanar gizo

Yayin da wasu masu garkuwa da mutane ke sakin jama'a bayan sun karba kudi hannu da hannu, sabon salon da yanzu masu garkuwa da mutanen suka dauka shine bukatar a tura kudi ta asusun banki.

A watan Afirilu, tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, Kingsley Moghalu, ya zargi cewa 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane sun fara bukatar kudin fansa da kudin yanar gizo wato cryptocurrencies.

Duk da bai banbance wacce kungiyar bace ke amfani da wannan salon, tsohon ma'aikacin bankin ya ce hakan ta nuna akwai bukatar sake dubawa tare da tsara kasuwar kudin yanar gizo a duniya.

Wasu 'yan Najeriya sun koka da yadda bankuna basu bada hadin kai wurin bankado 'yan ta'adda da ke damfarar jama'a ta hanyar amfani da asusun bankuna.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: Hatsarin mota ya hallaka mutane da dama a hanyar zuwa Minna

Hamisu Ibrahim, wani mazaunin Abuja ya bada labarin yadda 'yan canji a bankin suka sa yayi asarar kudinsa ga 'yan ta'adda.

Wani masani a harkar kudi, Umar Yakubu, ya ce gano miyagu da suka yi amfani da tsarin bankuna bashi da wuya, sai dai idan ba a so yin hakan ba.

Yadda 'yan bindiga suka sa muka biya kudin fansa ta banki

A ranar Laraba, 16 ga watan Yuni, 'yan bindiga sun dauke wata mata mai suna Aminat Adewuyi da wasu mutum hudu a Madalla yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa fitacciyar kasuwar Ibrahim Babangida dake Suleja, jihar Neja.

Daily Trust ta tattaro cewa 'yan uwan wadanda aka sace sun biya kudi har N500,000 da N1,000,000 ga wani asusun banki wanda miyagun suka bada lambar shi.

Wani dan uwan Amina, wanda ya bukaci a adana sunansa, ya ce bayan sun kammala ciniki da miyagun, sun bukaci a saka musu kudi ta asusun banki a maimakon a kai musu shi kai tsaye.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda Huɗu a Enugu

A wani labari na daban, Sarkin Muri, Alhaji Abbas Nijidda Tafida ya samu ganawa da shugabannin Fulani a fadarsa dake Jalingo kuma yayi kira garesu da su tsamo 'yan ta'adda dake cikinsu.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki shida da sarkin ya ja kunnen 'yan ta'addan dake cikin Fulani makiyaya dasu daina aiwatar da ta'addancinsu.

Taron da ya samu halartar Hardo, Jauro da sauran shugabannin kungiyoyin Fulani, an yi shi ne domin samo mafita kan miyagun al'amuran makiyaya, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel