Labari mai zafi: Kungiyar ASUU za ta iya komawa dogon yajin-aikin da ta dakatar a 2020

Labari mai zafi: Kungiyar ASUU za ta iya komawa dogon yajin-aikin da ta dakatar a 2020

  • Shugaban Kungiyar ASUU na ATBU ya fara maganar yiwuwar shiga yajin-aiki
  • ASUU ta zargi Gwamnati da kin cika duk alkawuran da aka yi a Disamban 2020
  • Maganar IPPIS ta na cikin sabanin Gwamnatin Tarayya da Malaman Jami’ar

Kungiyar ASUU ta malaman jami’a, ta na barazanar cigaba da yajin aikin da ta dakatar a baya a kan wasu sabani da ta samu da gwamnatin tarayya.

Punch ta ce shugaban kungiyar ASUU na jami’ar, Abubakar Tafawa Balewa watau ATBU da ke jihar Bauchi, Dr. Ibrahim Inuwa, ya bayyana wannan.

Dr. Ibrahim Inuwa ya yi wannan bayani ne yayin da ya zanta da wasu manema labarai a babban ofishin kungiyar da ke garin Bauchi a ranar Lahadi.

Ibrahim Inuwa ya ke cewa sun janye yajin-aiki a 2020 ne bayan an cin ma yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar ASUU.

Shugaban kungiyar malaman ya ce watanni bakwai da sa-hannu a yarjejeniyar, gwamnati ba ta ta iya cika mafi yawan jerin alkawuran da ta dauka ba.

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

Kungiyar ASUU
Wakilan ASUU da 'Yan Majalisa Hoto: myschoolnews.com.ng
Asali: UGC

Rahoton ya ce a cikin alkawura takwas da wakilan gwamnatin tarayya suka yi, biyu aka iya cika wa.

Korafin da kungiyar ASUU ta ke yi a lokacin sun hada da, kara kudin gudanar da aikin jami’o’i, gibin albashi, da kafa kwamitocin binciken jami’o’in jiha.

Har ila yau, Dr. Inuwa ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba ta maye gurbin manhajar IPPIS da UTAS da malaman jami’ar suka kirkiro ba.

“Maganar albashi da kwamitin duba jami’o’in gwamnatin tarayya kadai aka iya duba wa.”

Malamin ya ce kwamitin da zai duba yarjejeniyar 2009 bai gama aikin da ya kamata ya karkare cikin watanni biyu ba, sannan ana zaftare albashinsu ta IPPIS.

Tun Disamban shekarar 2020, ASUU ta yarda ta koma bakin-aiki, bayan an rufe jami’o’i na watanni.

A makon da ya gabata ne aka ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya samu matsayi a ISCP da Jami’ar nan ta CUC da ke kasar Uganda.

Kara karanta wannan

Kanu da Igboho: Kungiyar arewa ta dau zafi, ta bayyana abun da ya kamata FG ta yi wa ‘yan bindiga da makiyaya

Jonathan ya zama Shugaban kungiyar ISCP da aka kafa domin kawo zaman lafiya a nahiyar Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel