Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno

Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno

  • Dakarun sojojin Nigeria na Operation Hadin Kai sun kama wani mutum da ya yi ikirarin shi dan sanda ne dauke da makamai
  • An kama mutum da ya ce sunansa Ebenezer Ojeh dauke da harsashi 220, gurnetin hannu, wuka da wasu makamai ne a hayar Maiduguri zuwa Damaturu
  • Majiya ta bayyanan sirri ta ce mutumin yana dauke da unifom din yan sanda mai sunan Ebenezer Ojeh amma ba a tabbatar da ko shi wanene ba da abin da ya kawo shi Borno

Dakarun sojojin Nigeria na Operation Hadin Kai sun kama wani da ake zargi da laifi, Ebenezer Ojeh, wanda ya yi ikirarin cewa shi dan sanda ne mai mukamin saja dauke da harsasai da gurneti a jihar Borno, The Cable ta ruwaito.

PRNigeria ta ruwaito cewa Dakarun Sojoji na 154 Battalion Ngamdu karkashin jagorancin mukadashin kwamanda Manjo D.Y. Chiwar ne suka kama wanda ake zargin a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sojoji Sun Cafke Wani Jami'in Dan Sanda da Tarin Alburusai da Gurneti a Borno

Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno
Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti Da Wasu Kayayyaki a Borno. Hoto: PRNigeria
Asali: Facebook

Ta yaya aka kama wanda ake zargin?

Wani majiya daga sashin tattara bayanan sirri ya ce:

"An kama Ebenezer Ojeh ne a shingen binciken jami'an tsaro saboda yanayin alamun rashin gaskiya da aka lura da shi tun lokacin da ya hau motar haya ta Borno Express domin zuwa Abuja.
"Bayan an bincika jakarsa, an gano kimanin harsashi 220 masu tsawon 7.62mm, gurneti na hannu guda daya, karamar wuka da wasu kayayakin.
"Yayin da sojoji ke masa tambayoyi, Ojeh ya yi ikirarin cewa shi jami'in rundunar yan sandan Nigeria ne a sashi na musamman ta SWAT a jihar Rivers.
"Duk da cewa unifom da abin suna da ke hannunsa na dauke da sunan wani Saja Ebenezer Ojeh mai lamba 456647, ba mu riga mu tabbatar ko shi wanene ba da abin da ya kawo shi Borno tunda ya yi ikirarin cewa a jihar Rivers ya ke aiki."

Kara karanta wannan

Ba aikin mu bane dakatar da masu fafutuka , sai dai ba za mu laminci rikici ba - Rundunar Sojoji

Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno
Hotunan gurneti, harsashi, wuka da wasu kayayyaki da sojoji suka kama hannun wani da ya yi ikirarin shi dan sanda ne. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno
Hotunan unifom din dan sanda da aka kama hannun wani mutum da ake zargin dan sandan bogi ne a Borno. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Wani majiyar ta sojoji ta shaidawa The Cable cewa ana zargin dan sandan bogi ne.

Majiyar ta ce:

"Bai kamata ya yi tafiya da makamai ba. Abin zargi ne. Babu dan sandan da aka bawa izini ya rika tafiya da ko da harsashi daya ne. Kuma da aka tsayar da shi, ya yi kokarin tserewa kafin aka taro shi."

An mika wanda ake zargin da kayayyakin da aka kama shi da su ga hedkwata ta sector 2 na Operation Hadin Kai domin zurfafa bincike.

Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Rahoton da The Guardian ta wallafa ya nuna cewa Hukumar yan farin kaya DSS tana farautar dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo.

Hukumar ta DSS ta sanar da hakan ne a daren ranar Alhamis 1 ga watan Yuli yayin taron manema labarai inda ta tabbatar cewa tawagar jami'an tsaro sun kai samame gidan Igboho da ke Soka a Ibadan, jihar Oyo.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiya Ta Shawarci Sunday Igboho Da Nnamdi Kanu Su Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa

An fahimci cewa cewar yan sandan sirrin na Nigeria sun tabbatar da cewa sun bindige mutum biyu cikin masu aiki tare da Igboho yayin da sauran aka ci galaba a kansu aka kama su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel