Ku tsamo dukkan miyagun dake cikinku, Sarkin Muri ga shugabanni Fulani

Ku tsamo dukkan miyagun dake cikinku, Sarkin Muri ga shugabanni Fulani

  • Sarkin Muri na jihar Taraba, yayi muhimmin taro da shugabannin kungiyoyin Fulani makiyaya a jihar
  • Ya yi kira ga shugabannin da su tsamo miyagun makiyaya dake cikinsu masu bata sunan Fulani a kasar nan
  • Kamar yadda shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar, Sahabi Tukur yace, sarkin yace dole ne a tsamo bara-gurbi daga cikinsu

Sarkin Muri, Alhaji Abbas Nijidda Tafida ya samu ganawa da shugabannin Fulani a fadarsa dake Jalingo kuma yayi kira garesu da su tsamo 'yan ta'adda dake cikinsu.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki shida da sarkin ya ja kunnen 'yan ta'addan dake cikin Fulani makiyaya dasu daina aiwatar da ta'addancinsu.

Taron da ya samu halartar Hardo, Jauro da sauran shugabannin kungiyoyin Fulani, an yi shi ne domin samo mafita kan miyagun al'amuran makiyaya, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Rashin tashin bam ko 1 yayin sallah alamace ta dawowar ingancin tsaro, Fadar Buhari

Kara karanta wannan

Rashin tashin bam ko 1 yayin sallah alamace ta dawowar ingancin tsaro, Fadar Buhari

Ku tsamo dukkan miyagun dake cikinku, Sarkin Muri ga shugabanni Fulani
Ku tsamo dukkan miyagun dake cikinku, Sarkin Muri ga shugabanni Fulani. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan sanda sun bankado yunkurin harin 'yan bindiga, sun ceci mutum 8 a Katsina

Daily Trust ta tattaro cewa sarkin yace umarninsa ba ga makiyaya bane kadai, yayi su ne ga dukkan miyagun dake cikinsu da ke garkuwa da mutane da sauran miyagun al'amura.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Taraba, Sahabi Tukur, wanda ya halarci taron ya sanar da Daily Trust cewa sarkin ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake samun al'amuran garkuwa da mutane a cikin Fulani.

Ya ce Sarkin wanda shima bafulani ne yace baya jin dadin yadda garkuwa da mutane ke da alaka da Fulani kuma ya ja kunnen miyagu daga cikinsu inda yace dole a tsamo su kuma a yi maganinsu kamar yadda doka ta tanadar.

Sahabi Tukur ya kara da cewa dole ne dukkan shugabannin Fulani su mayar da hankali wurin tsarkake Fulani makiyaya.

"Dole ne mu tsamo dukkan miyagun dake cikinmu kuma mu mayar da hankali wurin dawo da sunan Fulani wanda a hankali yake bacewa saboda miyagun dake cikinmu masu garkuwa da mutane da sauran miyagun al'amura," Sarkin yace.

Kara karanta wannan

‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo kan kamun Igboho

Amma kuma Sahabi ya bayyana cewa za a kafa kwamitoci daban-daban domin shawo kan matsalar ta'addanci da wasu Fulani ke yi tare da dawo da martabarsu a idon duniya.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga 'yan siyasa da kada su yi wa mulkinsa karya domin samun hawa kujerun siyasa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Shugaban kasan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis, yayin da ya karba bakuncin wasu gwamnonin da aka zaba karkashin jam'iyyar APC a Daura, jihar Katsina.

Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, Buhari ya bukaci masu tattara tarihi da su yi adalci wurin ajiye tarihin mulkinsa, "ballantana wurin nunawa masu zabe da su yi zabi mai kyau na shugabanni a kasar nan."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel