Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Yan Sanda a Jihar Kaduna

Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Yan Sanda a Jihar Kaduna

  • Jami'an yan sanda sun samu nasarar fatattakar wasu yan bindiga da suka yi kokarin kai musu hari a hedkwatarsu
  • Yan bindigan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi da isarsu amma basu ji da daɗi ba daga hannun yan sandan dake bakin aiki
  • Hukumar yan sandan jihar Kaduna ta fara gudanar da binciki ta hanyar wasu shaidu da ta gano a wurin faffatawar

Rundunar yan sanda ta jihar Kaduna tace jami'anta sun daƙile wani hari da yan bindiga suka yi kokarin kaiwa hedkwatar yan sanda dake Maraban Jos, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kakakin yan sanda na jihar, ASP Muhammed Jalige, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Asabar a Kaduna.

Yace harin wanda aka kai ranar 23 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 11:00 na dare, ya kunshi adadi mai yawa na yan bindiga, waɗanda suka zo a cikin motar sharon guda uku.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke 'yan sa kai 7, sun bankawa motar yaki wuta

Yan sanda sun daƙile harin yan bindiga a Kaduna
Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Yan Sanda a Jihar Kaduna Hoto: financialnigeria.com
Asali: UGC

A cewarsa, yan bindigan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin su samu damar kutsawa cikin hedkwatar, amma jami'an dake aiki suka maida martani cikin gaggawa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

An yi musayar wuta ta tsawon lokaci

A jawabin ASP Jalige, an ɗauki mintuna da dama ana musayar wuta tsakanin maharan da jami'an yan sanda, inda daga bisani yan bindigan suka tsere tare da muggan raunukan harbi.

Yace: "Abu mara daɗi shine sufetan yan sanda ɗaya da kwanstabul biyu sun samu raunuka kala daban-daban, amma yanzun haka ana kulawa da lafiyarsu a asibiti."

Hukumar yan sandan ta ƙara da cewa an kaddamar da bincike game da lamarin domin gano waɗanda suka kai harin.

Ta kara da cewa za'a yi amfani da wasu shaida da aka gano a wurin da lamarin ya faru domin kamo yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel