Cikin mako guda: 'Yan bindiga sun kashe mutum 48, da kona sama da gidaje 300 a Kaduna

Cikin mako guda: 'Yan bindiga sun kashe mutum 48, da kona sama da gidaje 300 a Kaduna

  • ‘Yan bindiga sun kashe mutum fiye da 48 a Jihar Kaduna tare da kona gidaje da dama a yankin Atyap
  • Wani shugaban al’ummar Atyap ya ce hare-haren ‘yan bindigar sun shafi kauyuka 12
  • Ya roki al’ummomin yankin da dinke barakar da ke tsakaninsu

Akalla mutum 48 aka kashe tare da kona gidaje sama da 300 inda ake zargin wadansu ‘yan bindiga da ake jin cewa ‘yan fashi ne a Karamar Hukumar Zango Kataf da ke cikin Jihar Kaduna suka hallaka mutanen.

An ce 'yan bindigar sun kai harin ne a cikin mako guda.

Shugaban kungiyar ci gaban kabilar Atyap, Samuel Achie, ya ce hare-haren da aka kai cikin tsawon wasu kwanaki a wasu kauyuka 12 da ke karkashin masarautar Katafawan, inda suka raba mutum fiye da dubu daya da muhallansu tare da jikkata wadansu da dama.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Alhamis a Kaduna, rahoton ChannelsTV.

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

Yace:

"Muna bukatar zaman lafiya fiye da kowane abu yanzu kuma mun dogara ga Allah cewa za a dawo da zaman lafiya a nan," .
“Ya kamata mu dauki kanmu a matsayin ‘yan uwan juna. Bafulatani dan uwa ne ga mutumin Ita, shi ma dan kabilar Ita hakan ya dace ya yi; sannan Bahaushe shi ma ya yi da mutumin Ita din hakan.
A lokacin da muka fara ganin kanmu hakan, kuma muka fara aiki a matsayin 'yan uwa maza da mata, babu wani dan uwa da zai so ya dauki makami a kan dan uwansa.”

'Yan bindiga sun kashe mutum 48, da kona sama da gidaje 300 a Kaduna
Cikin mako guda: 'Yan bindiga sun kashe mutum 48, da kona sama da gidaje 300 a Kaduna
Asali: Twitter

Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kawo musu dauki domin dakatar da kisan gillar kafin 'yan bindigar su gama da mutanen yankin.

Kauyukan da abin ya shafa sune Kibori da Magamiya 1 da 2, Matei da Makarau da Ungwan Rohogo da Ungwan Jaba da Abuyap da Jankasa da Ma-gata, Warkan da Kachechere.

Maharan sun haifar da mummunan lamarin jin kai a cikin kauyen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel