Zan iya ziyartar Daura duk makonni biyu kuma babu wanda zai iya hana ni, Buhari

Zan iya ziyartar Daura duk makonni biyu kuma babu wanda zai iya hana ni, Buhari

  • Shugaban kasa Buhari ya kasance a mahaifarsa, Daura a jihar Katsina don bikin Eid-el-Kabir na bana
  • Bayan bukukuwan, shugaban na Najeriya ya ziyarci fadar mai martaba Sarkin Daura, Dr. Umar Faruk Umar
  • Shugaban kasar ya nuna nadamar cewa ba zai iya ziyartar mahaifarsa ba kamar yadda yake so saboda matsalolin tsadar rayuwa da tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai iya zuwa mahaifarsa, Daura, jihar Katsina, duk makonni biyu idan yana so kuma babu wanda zai iya hana shi.

Amma, ya ce akwai abubuwan da za a yi la’akari da su kamar tsadar zirgga-zirgar shugaban kasa da kuma fallasa jami’an tsaro zuwa ga yanayi, PM News ta ruwaito.

Zan iya ziyartar Daura duk makonni biyu kuma babu wanda zai iya hana ni, Buhari
Buhari ya ziyarci sarkin Daura Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

A cewar Buhari, zai fi so ayi amfani da kudin yadda ya kamata kamar inganta makarantu, dakunan shan magani da asibitoci.

Shugaban kasar ya yi wannan bayanin ne a ranar Juma’a, 23 ga watan Yuli, lokacin da ya kai wa mai martaba Sarkin Daura, Dokta Umar Faruk Umar, ziyara a fadarsa.

Kara karanta wannan

Rashin tashin bam ko 1 yayin sallah alamace ta dawowar ingancin tsaro, Fadar Buhari

Ya lura cewa an san mutanensa da noma kuma yana da gonarsa a Daura.

Da yake nuna nadama game da rashin iya ziyartar danginsa akai-akai, ya ba su tabbacin cewa zuciyarsa na tare da su.

Buhari ya ceci Najeriya

A nashi bangaren, Mai martaba Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, ya ce Najeriya ta yi sa’a da samun Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa a irin wannan lokaci.

Basaraken ya ce abubuwa "da sun kasance da wahala matuka" idan da a ce ba Buhari ba ne yake jan ragamar mulkin kasar.

Ya yi magana ne a ranar Juma’a, 23 ga watan Yuli, lokacin da shugaban kasar ya ziyarce shi a fadarsa da ke Daura, jihar Kastina, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa jami'an Sojoji babban kyautar Sallah lokacin bikin Eidul Adha da yayi a mahaifarsa, Daura, jihar Katsina, Arewa maso yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Hakazalika shugaban kasan ya yiwa Matasa masu bautar kasa a Daura kyautar Bijimai biyu, buhuhunan shinkafa da makudan kudi yayinda suka kai masa ziyarar ban girma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel