Rimingado zai yi karar likitan da ya bashi shaidar asibiti ta bogi

Rimingado zai yi karar likitan da ya bashi shaidar asibiti ta bogi

  • Shugaban PCACC da aka dakatar, Muhuyi Magaji Rimin Gado zai maka Dr Bayo Ayodele a kotu
  • Hakan ya biyo bayan rahoton lafiyarsa na bogi da likitan ya bayar har ya gabatar ga majalisar jihar
  • Rimin Gado ya bukaci likitan yayi gaggawar wanke shi a gaban majalisar jihar cikin awanni 48 ko ya fuskanci hukuma

Shugaban PCACC na jihar Kano wanda aka dakatar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, yana shirin kai karar Dr Bayo Ayodele, likitan da ya bashi rahoton likita na bogi wacce ya gabatar gaban majalisar jihar.

Daga baya babban asibitin kasa dake Abuja sun musanta rahoton, Daily Trust ta ruwaito

Kamar yadda hukumar asibitin ta bayyana, ba daga asibitin rahoton yazo ba kuma basu da wani ma’aikaci mai suna Ayodele.

KU KARANTA: 'Yan sa kai zasu jagoranci yaki da 'yan bindiga a Sokoto, Tambuwal

Rimingado yayi karar likitan da ya bashi shaidar asibiti ta bogi
Rimingado yayi karar likitan da ya bashi shaidar asibiti ta bogi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Majalisar jihar Kano ta gayyaci Rimin Gado don ya bayyana gaban kwamitin wucin gadinta don bincike akan zargin da ake masa a ranar Laraba,14 ga watan Yulin 2021 amma ya ki zuwa sakamakon rashin lafiyarsa har da gabatar da rahoton asibiti.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Sai dai a korafin da RiminGado ya baiwa Dr Ayodele, ma’aikacin NCCE, Abuja, ya bashi sa'o'i 24 ya warware kullin da ya hada ko kuma ya fuskanci hukuma, The Nation ta wallafa.

Kamar yadda korafin yazo: “...Sakamakon bayar da rahoton asibiti na ranar 7 ga watan Yulin 2021 da ka sanya hannu daga babban asibitin tarayya dake Abuja inda ka bayyana sakamakon gwajin jini, bayan gida da fitsari na ranar 12 ga watan Yulin 2021.

“... Bayan tashin wannan kurar, muna umartarka da kayi gaggawar yin wadannan abubuwan da muka bukata.

“Kayi gaggawar bayyana wa ‘yan majalisar jihar Kano cewa gaskiya ne rahoton lafiyata da ka bayyana a takarda.

“Sannan wajibi ne ka rubuta takarda cikin sa'o'i 48 ka gabatar ga majalisar akan rashin lafiyata.

“Idan ka ki yin hakan kuma cikin kwana biyu zaka fuskanci hukuma.”

An dakatar da RiminGado farkon watan nan daga majalisar jihar Kano sannan an maye gurbin shi da Barrister Mahmoud Balarabe a matsayin shugaban PCACC na rikon kwarya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu a Kano ta haramtawa majalisar jiha binciken Rimingado

KU KARANTA: Da duminsa: Kotu ta umarci DSS da su gabatar da mukarraban Igboho 12 da suka tsare

A wani labari na daban, wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe 'yan sa kai 7 a wani hari da suka kai garin Dansadau dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun sanar da Daily Trust cewa miyagun 'yan bindiga sun kutsa yankin wurin karfe 3 na dare kuma sun je wuraren da suka yi niyya.

Sun dinga harbi a iska kuma daga nan suka shiga wasu gidaje kuma suka kwashe mutane 13 da suka hada da mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel