Bana Bukatar Ko Sisin Kobo Daga Hannunku, Shugaba Buhari Ga Yan Kwangila

Bana Bukatar Ko Sisin Kobo Daga Hannunku, Shugaba Buhari Ga Yan Kwangila

  • Shugaba Buhari ya gargaɗi yan kwangila da cewa baya bukatar cakin kuɗi daga hannunsu
  • Shugaban yace kamata yayi su koma gida domin tallafawa al'ummar su bawai ma'aikatan gwamnati ba
  • Buhari yace yana sha'awar zuwa Daura duk bayan mako biyu amma dole yake hakura

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira ga waɗanda suka amfana da kwangilar gwamnati da su maida hankali wajen abinda a ka sa su, maimakon su dinga kokarin kaiwa wasu ɗai-ɗaikun jami'an gwamnayi kyaututtuka, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Buhari yayi wannan jawabin ne a Daura, jihar Katsina, ranar Jumu'a yayin da ya ziyarci Sarkin Daura, Dr. Umar Faruk Umar.

Buhari yace: "Bana bukatar ko naira daga hannunku, kuje ku tallafawa jama'an yankin ku maimakon ku zo kuna baiwa wasu ma'aikatan gwamnati."

"Bamu bukatar kuɗi daga kowane mutum ko ƙungiya domin saka mana kan wata alfarma da muka yi. Ku rinka tunawa da abinda ya rataya a wuyanku."

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

Shugaba Buhari, Sarkin Daura da Yusuf Buhari
Bana Bukatar Ko Sisin Kobo Daga Hannunku, Shugaba Buhari Ga Yan Kwangila Hoto: @Buharisallau
Asali: Instagram

Mu manoma ne kuma inason Noma

Shugaban ya ƙara da cewa yana son zuwa Daura lokaci bayan lokaci, amma saboda kuɗin da ake kashewa wajen tafiya da kuma takurawar jami'an tsaro ta sa yake hakura.

Buhari ya bayyana cewa a ko ina ya tsinci kansa zuciyarsa da tunaninsa tana kan mutane, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

"An san mu da noma, kuma ina son inyi noma, zan so in rinka zuwa Daura duk mako biyu, amma kuɗaɗen da ake kashewa suna da yawa," inji shi.

Najeriya kasa ɗaya

Shugaban yace amincewar Allah tasa har yanzun Najeriya take a dunkule, inda baya matsaloli suka janyo yakin basasa na tsawon watanni 30.

Yace: "Muna ƙara godiya ga Allah da ƙasar mu take a dunkule. Daga ranar 12 ga watan Janairu, 1966 Najeriya ta shiga rikicin siyasa. Mun shafe watanni 30 ana yakin basasa.."

"Zamu cigaba da godiya ga Allah da yasa muke kasa ɗaya, mun kara jinjina ga mutanen da suka nuna sha'awar mu cigaba da kasancewa ɗaya."

Kara karanta wannan

Ku Mun Adalci Wajen Rubuta Nasarori Na, Shugaba Buhari Ga Marubuta Tarihi

Jawabin Godiya

A jawabinsa, mai martaba sarkin Daura, ya yi wa shugaba Buhati godiya bisa kokarinsa na ziyartar mahaifarsa duk da aikace-aikacen da yake da shi.

Yace: "Kawo ziyara Daura yana ƙara bayyana kyawawan ɗabi'unka wanda muke alfahari da su. Ina mai tabbatar maka da cewa Maza, mata da ƙananan yara a shirye suke su tarbe ka kuma suna maka addu'a."

Asali: Legit.ng

Online view pixel