Tsohon Shugaban Najeriya, Jonathan ya sake samun wasu manyan mukamai a Duniya

Tsohon Shugaban Najeriya, Jonathan ya sake samun wasu manyan mukamai a Duniya

  • Dr. Goodluck Jonathan zai rike Majalisar ISCP mai kokarin kawo zaman lafiya
  • A shekarar 2019 kungiyar UPF ta kafa International Summit Council for Peace
  • Jam’iyyar PDP ta taya tsohon shugaban Najeriyar murna, ta ba shi shawarwari

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya zama sabon shugaban majalisar International Summit Council for Peace da aka fi sani da ISCP.

Jaridar Daily Trust ta ce jam’iyyar PDP mai hamayya ce ta bada wannan sanarwar a wani jawabi da ta fitar a jiya, Alhamis, 22 ga watan Yuli, 2021.

An kafa majalisar International Summit Council for Peace domin wanzar da zaman lafiya a Afrika.

Rahoton ya ce tsofaffin shugabannin kasashen Duniya da mataimakinsu ne a wannan kungiya da Universal Peace Federation ta samar a 2019.

Jam’iyyar PDP ta taya shugaban na ta murnar samun wannan babban matsayi, ta yi kira gare shi ya yi amfani da sanin aikinsa wajen jan ragamar ISCP.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Mai magana da yawun bakin PDP, Mista Kola Ologbondiyan, ya fitar da wannan jawabi, ya ce an zabi Jonathan saboda irin yunkurin kawo zaman lafiyansa.

“Jam’iyyarmu ta na mai tabbacin cewa tsohon shugaban kasa Jonathan zai yi amfani da kware wa da sanin aikinsa da manufofin jam’iyyarmu wajen wannan sabon aiki na shi, na kafa turakun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kawo cigaba a Afrika.”

Tsohon Shugaban Najeriya, Jonathan ya sake samun wasu manyan mukamai a ketare
Jonathan da Shugaba Buhari Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Rahoton ya ce baya ga haka, PDP ta yi wa Goodluck Jonathan murnar zama sabon shugaban jami’ar Cavendish University, Uganda da aka fi sani da CUU.

“Jam’iyyar PDP ta na matukar farin ciki da tsohon shugaban kasa Jonathan zai rike matsayin da marigayi Kenneth Kaunda da Benjamin Mkapa suka rike.”

Ologbondiyan ya ce Jonathan ya samu wannan matsayi ne saboda yadda ya ke daraja neman ilmi da cigaban al’umma kamar yadda aka san jam’iyyarsu ta PDP.

Jiya Sanata Enyinaya Abaribe ya fadi abin da ya sa ya ki fito da Nnamdi Kanu bayan ya sulale, ya bar kasar, kuma ya zauna lafiya, ya ce kuma bai yi wata nadama ba.

Kara karanta wannan

PDP ta dumfari Kotun koli, ta ce a tsige Gwamna, ‘Yan Majalisun Zamfara da suka koma APC

Idan za a tuna, Enyinaya Abaribe ne ya tsaya a kotu aka bada belin Shugaban IPOB, amma ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel